Rundunar ko takwana ga yakunan da ake rikici
September 5, 2014Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta amince ta kafa wata runduna da za ta rika kai dauki cikin gaggawa a yankunan da ake fama da rikici. Babban sakataren NATO Anders Fogh Rasmussen ya ba da wannan sanarwa a gun taron kolin kungiyar kawancen tsaron a Newport da ke yankin Wales na kasar Birtaniyya. Wannan matakin na zama martani ga rikicin da ake da kasar Rasha game da yakin gabashin kasar Ukraine. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za su ci gaba da mara wa gwamnatin Kiev baya, inda ta kara da cewa: "Muna goyon bayan Ukraine, muna nuna mata zumunci. A shirye muke mu kara matsa kaimi na siyasa ta hanyar karin takunkumai. Amma muna kuma aike da sako cewa muna bukatar maslaha ta siyasa, kuma a shirye muke mu tattauna da Rasha."
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman