1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rundunar sojin Jamus ta janye rabin dakarunta da ke Mali

November 10, 2023

Sojojin da ke mulki a Malin ne suka bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta janye dukkan sojojinta dubu goma sha biyu da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar

https://p.dw.com/p/4YeKf
Hoto: Alexander Koerner/Getty Images

Rundunar sojin Jamus ta ce fiye da rabin sojojinta da ke cikin dakarun wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali sun bar kasar, inda ta bar guda 50 kadai a kasar, sai kuma guda 100 da ke Jamhuriyar Nijar har yanzu.

Karin bayani:Jaridun Jamus: Dakatar da zabe a Mali

Mai magana da yawun rundunar ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Jamus DPA cewa sun tsara kammala janye sojojinsu baki-daya daga kasar ta Mali daga nan zuwa karshen shekarar nan da muke ciki.

Karin bayani:Agajin Jamus a wasu kasashen Afirka ta Yamma

A cikin watan Yunin da ya gabata ne dai sojojin da ke mulki a Malin ne suka bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta janye dukkan sojojinta dubu goma sha biyu da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, bayan da ta fara dasawa da Rasha sakamakon kulla kawancen tsaro.