1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar hadakar yakar ta'addanci.

Abdoulaye Mamane Amadou
September 3, 2021

Sabuwar rundunar tsaro ta kasa da kasa mai hankoron tabbatar da tsaro "Takuba" ta soma aiki kafada da kafada da rundunar tsaron Faransa a yankin Sahel.

https://p.dw.com/p/3zrrq
Frankreich Mali - Militär Konflikte
Hoto: Frederic Petry/Hans Lucas/picture alliance

Rundunar Takuba za ta kumshi sojojin kasashen yankin ne da ma na ketare, kuma tuni tun a cikin watan Maris din wannan shekara ta soma aiki. Ga rahoton da Abdoulaye Mamane Amadou da karin bayani.

Kaptin Arthur ne ke bada umarnin dabarun yaki wa wasu sojojin rundunar da ke shirin kai sameme wa 'yan ta'adda da suka ji labarin cewa sun yi gungu su fiye da 20 a wani garin da ke kusa da inda sojojin suka ja daga.Karin Dole ne su hanzarta, saboda idan ba haka ba mayakan kan iya yiwa jama'a illa, domin wannan kuwa sojan na amfani ne da babura don kyalla ido a matakin farko a yankin, a gabaninsa wasu dakarun Estoniya na dafa wa askarawan baya. Kaptin Arthur kwandan bataliyar cewa yayi:

"Tare da hadin gwiwar sojan Mali mun dukufa don kakkabe wasu 'yan ta'addan da muka ji labari yau da kwana biyu sun kafa sansani a nan, mun tanadi duk wasu muhimman kayayakin bayanan sirri manufarmu ita ce na takaita kaifin illar hare-haren da abukan gaba kan iya yi."

Yankin Gao
Hoto: Philippe de Poulpiquet/LE PARISIEN/PHOTOPQR/MAXPPP/picture alliance

A hannu daya kuwa jiragen yakin kasashen Turai ne ke ci gaba da shawagi ta sararin samaniyar bataliya, hakan kuma dakarun na amfani da jirage maras matuka don lekon asirin halin da abukan gaba suke ciki, a kasa sojojin na kasashen ketare ne da na Mali ke ta aikin samamen kamar yadda Edrgar daya daga cikin sojan ya ce suna samun fahimtar juna.

"Akwai fahimtar juna sossai tsakaninmu musamman ma sojan Estoniya suna aiki tukuru kuma ga barkwanci sosai muna rarrabna ababen farinciki da dama tare da su, kuma muna koyon abbuwa da dama a tsakanimu."

Faransawa dai a yanzu ba su kadai ba ne dakarun nahiyar Turai da ke farautar yan jihadi a yankin sahel, kana kuma wani kwararre ta fanninj tsaro a Mali  Boubacar Haïdara ya ce wannan dabarar na karya ikrarin da Faransar ke yi na cewa tana yakin ta'addanci ita kadai, hakan kuma ya karya tasirin masu kin jinin sojan Faransa a yankin Sahel din din wanda suka soma gangamin yin hakan tun a shekarar 2019.

Rundunar Barkhane ta kasar Faransa
Hoto: AP Photo/picture alliance

Sai dai a cewarsa akwai lokuttan da dakarun kundun bala basa da wani cikakken tasiri

"Mun lura da cewa akwai raguwa ta sojan Faransa, kana kuma wannan ba wai don basu da wata kwarewa ne ba sai dai don matsalar da ake fuskanta a Mali wanda ya sha bamban da harkokin soja. Duk wani wanda za a kawo a yankin Sahel bana tsammanin zai tabuka wani abin fiye da Barkhane."

A cewar masanin dai ba wata rundunar da ka iya yin wani abin azo a gani fiye da ta Barkhane wacce ita din ma ta yi kuma aka gani wajen yakar kungiyar Alqa'ida da IS, sai dai har yanzu mayakan na ci gaba da mamaye wurare fiye da yadda ake zato, ba wata makawa kan wannan matsalar face hada wa da tattauanwa irin ta siyasa maimakon amfanii da karfin tuwo na soja a cewar masaninin.