1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwan bama-bamai a kasar Masar

January 24, 2014

Mutane shida sun hallaka a kasar Masar bayan da wasu bama-bamai hudu sukia tashi a Alkahira babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/1Awvj
Hoto: Reuters

Hare-haren bama-baman da aka kai a kusa da shalkwatar 'yan sanda da kuma wani gidan tarihi da ke Alkahira babban birnin kasar ta Masar, sun kara sanya fargaba kan ci gaba da samun harin kunar bakin wake daga 'yan yakin sunkuru a kan jami'an tsaro da ake ci gaba da samu tun bayan da sojojin kasar ta Masar suka kifar da gwamnatin zababben shugaban kasar Muhammed Mursi a wani abu mai kama da juyin mulki, inda kuma suke ci gaba da kokarin murkushe 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi dake marawa Murisin baya da karfin tuwo.

Gwamnatin rikon kwaryar kasar dake samun goyon bayan sojoji dai ta dade tana dora alhakin duk kan tashe-tashen hankulan da Masar din ta tsunduma a ciki tsahon watannin shidan da suka gabata, a kan 'yan kungiyar ta 'yan uwa Musulmi tare kuma da sanya kungiyar a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu