1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Carlos Alcaraz ya doke Novak Djokovic a Tennis

Suleiman Babayo AH
July 24, 2023

Kasar Jamus ta lallasa Moroko 6 da nema, sannan Japan ta yi laga-laga da Zambiya 5 da nema duk ana ci gaba da wasan mata na neman cin kofin duniya da kasashen New Zealand da Australiya suke daukan nauyi.

https://p.dw.com/p/4UJgA
Karawar Maroko da Jamus inda Jamus ta zura wa Maroko kwallo shida da nema
Karawar Maroko da Jamus inda Jamus ta zura wa Maroko kwallo shida da nemaHoto: Hannah Mckay/REUTERS

A wasan da aka gama ran Litinin, Jamus ta yi kaca-kaca da Moroko wajen cin kacar tsohon keke rakacau 6 da nema. Tun farko an zuba ido kan matan Moroko saboda yadda mazan suka taka rawar a zo a gani yayin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da ta gabata a kasar Katar wajen kai wa zuwa wasan kusa da na karshe. Idan har aka kammala wasannin Koriya ta kudu da Kwalambiya ne kadai za su kasance kungiyoyin da ba su riga sun yi wasa ba a gasar cin kofin kwallon kafar da ke gudana a Australiya da New Zealand. Kawo yanzu dai a kasashe 24 da suka kara, guda goma sun sami maki daya,10 ba su da ci ko daya yayin da hudu kuma suka yi kunen doki.

 

Max Verstappen ya lashe wasan tseren motoci na Formala

 Max Verstappen dan wasan tseren motoci
Max Verstappen dan wasan tseren motociHoto: ISSEI KATO/REUTERS

Max Verstappen shahararren dan wasan tseren motoci na Formala One ya lashe gasar da ta wakana a kasar Hangari cikin tawogar Red Bull. Wannan narasa ta kara karfafa matsayin Verstappen da tawogarsa a gasar tseren motocin ta duniya. A gasar nunkawan ruwa, Leon Marchand dan Faransa ya kafa tarihi lokacin nunkaya na mita 400 da ya kammala cikin mintoci 4 da dakika 2.50, a gasar da aka yi a Fukuoka da ke yankin kudu maso yammacin Japan. Haka ya nuna Marchand ya karya tarihin da dan Amirka, Michael Phelp ya kafa lokacin gasar Olympic a birnin Beijing na China a shekara ta 2008, inda ya kammala a mintoci 4 da dakika 6.

 

China ta ba da takardun zama 'yan kasa ga 'yan wasanni da dama

NO FLASH Basketball China Asienmeister 2011
Hoto: picture alliance/ZUMA Press

Shahararren dan wasan kwallon kwando na Amurka, Kyle Anderson ya karbi shaida zama dan kasar China, kamar yadda hukumar kula da wasan kwandon China ta sanar wadda ta  tabbatar da cewar dan wasan Kyle Anderson zai wakilci China lokacin wasan neman cin kofin kwallon kwando na duniya a wata mai zuwa. China ta ba da takardan zama 'yan kasa ga 'yan wasanni da dama cikin shekarun da suka gabata domin karfafa harkokin wasanni a kasar wadda take matsayi na biyu wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen duniya.

Carlos Alcaraz ya doke Novak Djokovic a wasan Tennis 

Carlos Alcaraz dan wasan Tennis
Carlos Alcaraz dan wasan TennisHoto: Kirsty Wigglesworth/AP/picture alliance

Novak Djokovic shahararren dan wasan tennis na duniya ya bayyana cewa yana bukatar karin lokaci na hutu wannan wasan na birnin London na kasar Birtaniya da aka kammala inda Carlos Alcaraz ya samu nasara kan Djokovic a wasan karshe. Haka ya janyo Djokovic cire kansa daga cikin wasan da aka tsara zai shiga a kasar Kanada. Dan shekaru 36 da haihuwa Djokovic wanda ya lashe manyan wasannin Tennis 23, ya ce bayan hutu zai fara shirye-shiryen shiga daya daga cikin manyan wasannin na Amurka da ke da tasiri.