Rwanda ta fara karbar 'yan cirani daga Libya
September 27, 2019Talla
Yawan mutanen da suka isa Ruwanda din dai ya kai 66 kuma daga cikinsu akwai mata da yara kanana , aikin kwashe 'yan ciranin daga Libiya ya biyo bayan wani roko da shugaba Paul Kagame ya yi tun a shekara ta 2017, inda ya bukaci kasar sa ta samarwa 'yan ciranin da suka fito daga kasashen Afirka mutsuguni.
A farkon wannan wata na Satumba ne Ruwanda ta rattaba hannu a yarjejeniyar hadin gwuiwa tsakaninta da kungiyar tarayyar Afirka watau AU da kuma hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya domin karbar masu neman mafakar da ke ragaita a Libiya.