1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwanda ta kori 'yan gudun hijiran Burundi

Salissou Boukari
April 1, 2018

Kimanin 'yan kasar Burundi 1,600 ne da ke gudun hijira a Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, kafin su koma a kasar Ruwanda a watan Maris da ya gabata ne, aka mayar da su ya zuwa kasarsu ta Burundi.

https://p.dw.com/p/2vLmk
Burundische Flüchtlinge in Ruanda
Hoto: S. Aglietti/AFP/Getty Images

A cewar hukumomin na Kigali, wannan lamari ya wakana ne, sakamakon kin aminta da 'yan gudun hijiran na Burundi suka yi a yi musu rejista na zamani da kuma shausahawar rigakafi ta sabili da dalillai na addini a cewarsu. Wadannan 'yan gudun hijira na Burundi da ke a garin Gashora na Kudu maso gabashin kasar ta Ruwanda, an tisa keyarsu ne ya zuwa garin Gasenyi-Nemba da ke kan iyakar kasar ta Burundi da Ruwanda a cewar shaidun gani da ido.

Baki daya dai kimanin 'yan gudun hijirar kasar Burundi 2,523 ne suka yi gudun  hijira ya zuwa Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, inda sakamakon fargabar mayar da su da karfin tuwo ya zuwa kasarsu ta Burundi, ta sanya suka yi ta sulalewa daga wannan kasa zuwa Ruwanda, inda suka nemi mafaka a ranar bakwai ga watan Maris da ya gabata.