1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sa in sa tsakanin Amirka da Iran

April 20, 2017

Sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson ya ce kasar Iran na ci gaba da zama barazana ga kasashen duniya, yana mai cewar babu alamun yarjejeniyar kasa-da-kasa kan makamin nukiliya za ta kai ga yin tasiri.

https://p.dw.com/p/2bZ2T
Rex Tillerson
Hoto: Picture-Alliance/AP Photo/I. Sekretarev

Rex Tillerson dai ya bayyana shakku kan manufofin kasar ta Iran dangane da yarjejeniyar da manyan kasashe suka cimma a birnin Vienna na kasar Austria a shekara ta 2015. Ya kuma zargi kasar da yin amfani da kudade da 'yan tawaye wajen rurruta wutar rigima da ma tauye hakkin jama'a musamman wadanda ke adawa da gwamnati. Kasar ta Iran dai ba ta yi watsi da ilahirin matsayin ta kan yarjejeniyar ba, sai dai Tillerson na cewar kasar na jan kafa don haka zai iya zama barazanar gaske ga yankin larabawa dama duniya baki daya.