Amirka ta gargadi Rasha kan aniyarta
January 21, 2022Talla
Blinken ya bayyana haka ne a lokacin ganawarsu da sakataran harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov a Geneva. Ukraine na zargi Rasha da dada jibge dakarunta a kan iyakarta da Ukraine tare da ba da karin tallafin makamai ga 'yan aware na gabshin Ukraine na yankin Kirimiya. Gabashin na Ukraine na fama da yaki tun a shekara ta 2014 inda 'yan awaren ke kokarin ballewa wadanda ke samun goyon bayan Rasha.Taron na jami'an diplomasiyar manyan kasashen guda biyu da ke gudana a Geneva ana yin shi ne da nufin warware rikicin tsakanin Rashar da Ukraine. Rasha dai na bukatar ganin rundunar tsaro ta Nato ta janye dakarunta daga Bulgeriya da Romaniya gabannin cimma duk wani sulhu a kan Ukraine.