Sa-in-sa tsakanin sojojin Nijar da hadiman Bazoum
July 31, 2023A cikin sanarwa mai lamba 14 da majalisar mulkin soji ta CNSP ta fitar, ta zargi Hassoumi Massaoudou da ke zama ministan harkokin waje da Kanal Guire Midou babban kwamandan rundunar tsaro ta "Garde Nationale" da sanya hannu kan wata takarda da ke bai wa Faransa izinin kai farmaki a fadar shugaban kasa domin kwato Shugaba Mohamed Bazoum daga hannu masu garkuwa da shi.
Kakakin gwamnatin mulkin sojin Nijar kanal kamar dai yadda Amadou Adramane ya bayyana cewa:"A kokarin da take na samun hanyar da za ta ba ta damar yin amfani da karfin soja a Nijar, kasar Faransa da hadin gwiwar wasu ‘yan Nijar, ta gudanar da wani taro a hedikwatar rundunar sojoji ta "Garde Nationale" domin samun izini na siyasa da na soja da take bukata."
Sai dai yayin da take mayar da martini, jam'iyyar PNDS-Tarayya ta bakin kakakinta a nahiyar Turai Idrissa Wazir Dan Madaoua ta ce zargin ba shi da tushe da makama. Shi ma Lawael Sallaou Tsayyabou, shugaban kungiyar RODAHD da ke fafutikar kare dimoukradiyya cewa ya yi akwai alamar cewa sojojin da ke mulki sun rikice, kana akwai baraka a tsakaninsu.
Kame-kame na yawaita a PNDS-Tarayya
Ministan cikin gida Hamadou Adamou Soule ,ya nunar da cewa sabbin hukumomin mulkin soji na ci gaba da kamen ‘ya'yan jam'iyyar PNDS-Tarayya da abokanin kawancensu: A halin yanzu mutane kimanin 130 suka shiga hannu wadanda suka hada da Shugaban jam'iyyar na kasa Foumakoy Gado, da ministar ma'adanai Madam Ousseini Hadizatou Yacouba da Honnorable Kalla Moutari da ministan man fetur kana dan tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou, wato Maman Sani Mahamadou da ministan fasali Rabiou Abdou, da kuma ministan sufuri Alma Oumarou.