Sababbin wuraren tarihi a Afirka
Hukumar kula da kimiyya da ilimi da al'adu ta Majalaisar Dinkin Duniya UNESCO ta bayyana wasu sababbin wuraren tarihi a Afirka. Wasu wuraren tarihin na shirin bacewa. Muna maraba da sababbin shiga daga Afirka.
Thimlich Ohinga
Duwatsu a kan dutse, ba tare da wata kariya ba. Sun kasance a haka har tsahon sama da shekaru 500. Bangon duwatsu na Thimlich Ohinga ya kasance wajen adana kayan tarihi mai muhimmanci a gabashin Afirka. Sun cimma al'adun al'ummar da suka kasance a yankin Tafkin Victoria tun daga karni na 16. Hukumar UNESCO ta sanya Thimlich Ohinga guda daga wuraren tarihi na duniya a karshen watan Yunin 2018.
Tekun Turkana, Kenya
Tun tsahon shekaru Tekun Turkana ke cikin jerin wuraren tarihi na duniya. Sai dai a watan Yuni da Yuli na 2018, Hukumar UNESCO ta nunar da cewa tekun na Kenya na fuskantar barazana. Ruwan dam din Gibe III na kasar Habasha da kuma sauyin yanayi na barazana ga Tekun Turkana.
Asmara babban birnin Eritrea
Birnin Asmara na kan wani dogon dutse, da ake iya hango waje mai nisan sama da mita 2000 idan aka hau kansa. Daga shekara ta 1890 zuwa 1941 Eritrea na karkashin mulkin mallakar Italiya. Asmara ya kasance cibiyar Italiyawa daga bisani gwamnatin masu matsanancin kishin kasa ta Mussolini ta fadada birnin. Asmara na zaman guda daga wuraren tarihin da suka shiga UNESCO tun daga shekara ta 2017.
Tun zamanin mulkin mallaka
Duk wasu birane da suka kasance karkashin Italiya tun daga shekara ta 1893 na cikin wuraren tarihi na duniya. Daga cikinsu akwai gine-ginen gwamnati da wuraren kallo da masallatai da wuraren ibada. Cocin Katolika ta Iritiriya "Our Lady of the Rosary," na zaman guda daga wuraren tarihi na duniya baya ga zaman biranen da ke makwabtaka na Arbate Asmera da kuma Abbashawel.
Birnin Afirka na zamani
Gine-gine da aka kawata saboda kasuwanci sun dauki hankalin hukumar UNESCO a shekara ta 2017. Birnin Asmara ya kasance daga cikin biranen Afirka na zamani tun farkon karni na 20. Ya zamto guda daga cikin wuraren tarihi na duniya a tsarin Afirka.
Tsohon birni na Mbanza Kwango a Angola
Angola ma ta samu damar shiga sahun wuraren tarihi na duniya na UNESCO a karon farko a shekara ta 2017. Birnin Mbanza Kwango na kusa da kan iyakar kasar da Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango a Arewa maso Yammacin kasar. Ya taba zama babban cibiyar Kwango ta siyasa da addini daga karni na 14 zuwa na 19. A karni na 15, Turawan mulkin mallaka na Potugal sun fadada shi da gine-gine na duwatsu na Turai.
Coci mafi dadewa a Afirka?
Birnin ya yi fice a matsayin birnin 'yan Kathedral a karni na 16. Wasu 'yan Angola sun ce ita ce coci mafi dadewa a Afirka. A cewar hukumar UNESCO: Fiye da sauran birane a yankin Kudu da Saharar Afirka, birnin Mbanza Kwango na nuna alamun sauyin da Kiristoci da Turawan mulkin mallakar Potugal suka kawo.
Yankin al'adu na Khomani a Afirka ta Kudu
Yankin al'adu na Khomani na arewacin kasar, kusa da kan iyakarta da kasashen Botswana da Namibiya. A wannan yankin ne wajen shakatawa na kasar na Kalahari-Gemsbok yake. Yanayin kasar na nuna alamun rayuwar dan Adam a lokacin shekarar duwatsu. Wadannan alamu na da alaka da rayuwar makiyaya na Khomani-San.
Rayuwa mai birgewa
Wurin tarihin na duniya na duba tarihin 'yan gudun hijira, abin dogaro na rayuwa da ma tarihin San, da ya rayu cikin sahara. A cewar UNESCO bangaren al'adun wajen, shaida ce ta sauyawar rayuwar da ta gudana tsahon dubban shekaru, kuma har yanzu tana ci gaba da sauyawa.
Wajen shakatawa na gabar ruwan Sudan
Sanganeb-Atoll da ke Tekun Bahar Maliya ya zamo cikin wuraren tarihi na hukumar UNESCO tun a shekara ta 2016. Ya kasance kimanin kilomita 25 da gabar ruwan Sudan. A wajen akwai wurin shakatawa na Dungonab da tsibirin Mukkawar, kilomita 125 daga gabar ruwan Bur ta Sudan. Yankin yana da yalwar bishiyoyi da ciyayi, kana wajen shawagin tsuntsaye da manya-manyan kifaye da kuma kunkuru.
Dutsen Ennedi na Chadi
Dutsen Ennedi na yankin Arewa maso Gabaashin Chadi ya zamo guda daga cikin wuraren tarihi na duniya a shekara ta 2016. Ruwa da iska sun sanya dutsen ya zamo abin sha'awa da birgewa. Dutsen Ennedi na zaman babban dutse a yankin Sahara: An yi zane-zane da dama na dutsen da ke nuna abin da ya faru a baya.
Kogin Okavango na Baswana
A arewacin Baswana Kogin Okavango na gudana zuwa dubban kilomitoci, kuma ruwan na tumbatsa. Kogin na zaman gida ga dubban dabbobi da ke fuskantar barazanar karewa kamar su damusa da mugun dawa da zaki da kuma karnukan daji na Afirka. Cikin watan Yuli hukumar UNESCO ta samar da sababbin wuraren tarihi na duniya. Wurare biyu daga Afirka suke.