Sabani tsakanin Amirka da Rasha kan Assad
May 18, 2016Kasashen Rasha da Amirka da ke zama na gaba-gaba wajen jagorantar zaman tattaunawar sun kasa samun daidaito akan batun makomar shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad.
To sai dai kuma mahukuntan biranen Moskon da Washington sun amince su sanya idanu akan bangarorin da basa ga muciji da juna.
A ta cewar Jonh Kerry sakataren harkokin wajen Amirka, kasashen zasu dauki matakan da suka wajaba akan rikicin kasar ta Siriya daya kici yaki cinyewa.
Simon Mabom da ke zama malami a Jami'ar Lancaster cewa yake.
Ina ganin kalaman da Kerry yayi kalamai ne na harshen damo ta yin la'akari da nanata kalmar cigaba da karya shirin zaman lafiyar,kalaman na bayar da ma'ana daban -daban ga wadanda keda ruwa da tsaki a rikicin Siriya, to amma ina ganin wannan matakin na zuwa ne a daidai, kuma yunkuri ne na kaiwa ga wani mataki mai kyau.