1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani tsakanin 'yan jam'iyyar MNSD Nasara

November 7, 2013

A Niger jam'iyyar MNSD Nasara madugar jam'iyyun adawar kasar, ta mayar da martani a game da kamen wasu 'ya'yanta da gwamnatin kasar ta soma a jihar Maradi.

https://p.dw.com/p/1ADqQ
Hoto: DW

Biyo bayan matakin da wasu 'ya'yan jam'iyyar su ka dauka a cikin wanann jiha na kewaya laya a tsakanin yan majalisar dokokin kasar a wani mataki na neman taka birki ga wasu 'yan majalisar dokokin kasa na jihar masu da'awar baiwa gwamnati mai ci goyan baya duk da haramcin da uwar jamiyyar tasu ta yi masu. Saidai rukunin yan majalisar jam'iyyar da ke da wannn matsayi na marawa gwamnatin baya ya ce yana nan a kan bakansa, domin ba ya da wata fargaba dangane da wanann mataki na kewaya masu laya.

Wannan rikici na yayan jamiyyar ta MNSD Nasara madugar jam'iyyun adawar kasar ta Niger ya samo tushe ne yau kimanin watanni ukku da su ka gabata, lokacin da shugaban kasa ya yi ma wanann jam'iyya, dama wasu takwarorinta na bangaren adawa tayin shiga gwamnatin hadin kan kasa da ya ke son kafawa domin samun kwarin gwiwar fuskantar jerin kalubalai musamman na tsaro da kasar ta Niger ta ke fuskanta. To saidai bayan da da farko jamiyyar ta MNSD Naasara ta bayyana aniyarta ta karbar wanann tayi, daga bisani ta ci tuwan fashi bayan da aka kasa samun fahimtar juna tsakaninta da shugaban kasar da shugabannin yan adawar akan bukatarsu ta samun mukamin PM a cikin sabuwar gwamnatin. Tun daga wanann loakci ne aka soma samun rabuwar wutsiyar kaza tsakanin 'ya'yan jam'iyyar ta MNSD Nasara inda wasu 'yan jam'iyya masu da'awar cika alkawari su ka bada hadin kansu ga tayin shugaban kasar, tare ma da karbar mukamai na ministoci da manyan daraktocin kampanonin gwamnati, a yayin da a share daya rukunin wasu yan majalisar dokokin na wanann jam'iyya daga jihar Maradi su ka fito fili su ka bayyana goyan bayansu ga shirin shugaban kasar;To domin neman taka birki ne ga yinkurin wadannan bijirarrin yaya nata a farkon wanann wata na novamba wasu shugabanni da magoya bayan wanann jamiyya na cikin jahar Maradin su ka dauki matakin kewaya laya a tsakanin yan majalissar lokacin wani babban taron meting da su ka shirya a garin Maradin. To amma biyo bayan wanann mataki ne gwamnati ta kama wani daga cikin wadanda shugabanci wanann taro. Matakin da kuma ga bisa dukkan alamu matakin bai yima shugabannin jamiyyar dadi ba kamar dai yanda za ku ji daga Malam Ali Sabo, mataimakin shugaban jamiyyar na kasa kana shugaban jamiyyar ta MNSD Nasara na jihar Maradin:

"Yaron da aka kama mumu mai suna Gambo yau kwana ukku yana komisariya, kuma ga yanda mu ke ji suna da takarda ta jerin mutane sun kai ashirin da su ke so su kama saboda wanann taro da mu ak yi na maradi mu ka sa laya bisa kan diptoci mu ka ce tun da jamiyya su ka shigo to amana in har su ka kamawa milki Mahammadu Isufu mu ka ce akan laya;to MNSD Nasara ta kasa duka mun ce ma gwamnati a sake shi tun yanzu kuma in suna so ne su yi milkin kama karya to mun yi zama da su lokacin da mu aka yi kokowa kowa ya san kowa"

Mahamadou Issoufou
Shugaban Jamhuriyar Niger Mahamadou IssoufouHoto: picture alliance/dpa

Yan majalisar dokoki 17 ne jamiyyar adawar ta MNSD NASARA ta mallaka a cikin jahar ta Maradi kuma sai da masu sanya layar su ka kira sunan ko wani daga cikinsu kafin gitta matakin layar akansa. To saidai a wata fira da su ka yi da manema labarai yan majalissar dokokin jihar ta Maradi masu goyan bayan gwamnatin sun ce suna nan akan bakansu, kuma ba su da wata fargaba a game da matakin kewaya masu layar da su ka ce ba shi da wani tasiri a garsu. Honourable Elhaji Haruna Kane Dan Labo shine kakakin wadannan yan majalisa:

"Wallahi babu wani fargaba tun da kai ka san Allah bai zalinci kawai sai gaba na shi fadi;su wadannan da su ka sa alkur'ani da wadanda su ka sa hannu su alkur'ani zai ci saboda suna wasa da ayar Allah ne dan ba mu dauki kayan kowa ba haraka ce ta ga inda mu ke bada goyan baya su kuma ga inda su ka karbo kudi su ke bada goyan baya, kuma wadanda su ka sanya layar ba magoya bayamu ba ne domin wanda zai sanyalayar rasawa aka yi sa da aka dauko dan wata jamiyya aka bashi jikka 10 dan shi zo shi karanta takardar amma nan gaba in Allah ya ya yarda ka zo Maradi za ka ga magoya bayammu da yardar Allah."

Yanzu haka dai ko baya ga jamiyyar ta MNSD Nasara jam'iyyar Lumana Afirka ta Malam Hama Amadu wacce ta fice daga bangaran jam'iyyun da ke mulki domin komawa sabon kawancan jamiyyun adawa na ARDR na fuskantar irin wanann kalubale na kwararra 'ya'yanta zuwa cikin gwamnatin, abun da kuma ke ci gaba da haifar da karin rudani da cece-kuce a fagen siyasar kasar ta Niger a yau.

Seini Oumarou Vorsitzender der Partei MNSD im Niger Afrika
Shugaban jam'iyyar adawa ta MNSD Nasara a Jamhuriyar Niger Seini OumarouHoto: MNSD

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Umaru Aliyu