Sabanin ra'ayin Merkel da Trump kan Pyongyang
September 20, 2017Ta bayyana hakan ne a wata fira ta musamman da ta yi da tashar DW a wannan Laraba a ci gaba da tattaunawar da tashar take da shugabannin 'yan siyasar kasar ta Jamus a daidai lokacin da ake shirin gudanar da babban zabe a kasar inda ta ce hanyar diplomasiyya da ta matakin saka takunkumi su ne hanyoyi mafi a'ala wajen shawo kan wannan rikici.
Da kuma ta juya kan batun siyasar kasar Jamus musamman dangane da batun jam'iyyar AfD ta masu kyamar baki da wasu rahotanni ke cewa na kara samun magoya baya daga jam'iyyu masu mulki, Angela Merkel cewa ta yi:
"Kan wannan batu amsa ta a bayyane take cewa ni abin da ya dame ni shi ne shawo kan matsalolin jama'a a fannin kiwon lafiya da ilimi da kuma dagewa a kan kawo karshen halayen kyama da na tarzoma."
A ranar Lahadi mai zuwa ne dai ake gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar ta Jamus, inda shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ke sake tsayawa neman shugabancin gwamnatin kasar a karo na hudu.