1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin hare-hare a Kolofata na kasar Kamaru

Mouhamadou Awal Balarabe
June 2, 2017

Mutane bakwai sun rasa rayukansu a wasu tagwayen hare-hare da ake kyautata zaton cewar 'yan Boko Haram sun kai Kolofata da ke arewacin Kamaru.

https://p.dw.com/p/2e2a2
Kamerun Kolofata Selbstmordanschlag Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Wasu tagwayen hare-haren ta'adanci sun halaka akalla mutane bakwai tare da jikata fiye da wasu karin 20 a wani sansani na 'yan gudun hijira a Kolofata da ke Kuryar arewacin Kamaru. Shaidu sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga biyu da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka tada bam da ke daure a jikinsu. Dama dai garin na Kolofata ya fuskanci irin wannan hari a watan Satumban bara inda mutane tara suka rasa rayukansu.

Gwamnatin ta Kamaru ta tura da tankokin yaki a shekarun baya-bayannan don murkushe 'yan Boko Haram tun bayan da hare-haren suka fara zama ruwan dare.  Mutane dubu 15 ne suka rasa rayukansu a kasashen da ke kewayen tafkin Chadi tun bayan da kungiyar Boko Haram da ke da'awar kafa daular Musulunci ta fara kai hare-hare a wannan yank..