Sabbin matakai na kawar da kungiyar IS
September 27, 2015Talla
Mai magana da yawun Firaministan Iraki din haidar al-Abadi wato Saad al-Hadithi ya ce kasashen sun amice da girka wani kwamiti da zai maida hankali wajen musayar bayanai na sirri kuma tuni Iraki ta bada wanda zai wakilce ta.
Kwamitin inji al-Hadithi zai kuma sanya idanu ne kan irin motsin da dakarun IS din ke yi daga waje zuwa waje da kuma yin kokari na dakile irin karfin da suke da shi.
Gabannin wannan dai, Rasha ta aike da jiragen yakinta da dakaru Siriya kana shugaban Rasha din Vladmir Putin zai tattauna da wasu takwarorinsa musamman ma Barack Obama nan gaba kadan kan wannan batu.