Sabbin matakan tsuke bakin aljihu a Spain
July 11, 2012Firaministan Spain Mariano Rajoy ya bayyana wa majalisar dokokin ƙasar sa jerin sabbin matakan tsuke bakin aljihun da gwamnatin sa ke shirin aiwatar wa. Daga cikin matakan dai harda ƙarin kaso ukku cikin 100 akan harajin da gwamnati ke karɓa wanda a yanzu ya kai na kashi 21 cikin 100, kana da rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa da ƙarin Euro miliyan dubu ukku da dubu 500 ta hanyar soke alawus-alawus na kirsimeti ga ma'aikatan gwamnati kana da ragin kuɗin haraji ga waɗanda ke sayan gidaje.
Hakanan firaministan na Spain ya bayyana rage kuɗaɗen tallafin da hukumomi ke baiwa marasa aikin yi da kuma na jami'an ƙananan hukumomi. Firaminista Rajoy ya sanar da majalisar dokokin Spain cewar, ƙasar na fama da matsalar koma bayan tattalin arziƙi mafi muni a cikin tarihin ta, yana mai cewar matsalar za ta ci gaba har ya zuwa aƙalla shekara guda nan gaba.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou