Sabbin muradun Kabila a gabashin Kwango
August 17, 2016Gwamnati a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku a yankin gabashin kasar bayan wani harin da kungiyar 'yan tawaye ta ADF na Yuganda ta kai a garin Beni da ke a lardin Rwangoma a gabashin kasar inda suka kashe mutane sama da 42 a ranar Asabar.
Wannan rana ta kasance wata rana ta bakin ciki ga Edmond Masumbuko magajin garin Beni da ke cikin lardin na Rwangoma a gabashin Jamhuriyar ta Demokaradiyyar Kwango, wanda ya bayyana a gaban al'ummar a ranar Lahadi a lokacin da aka yi jana'izar wasu daga cikin wadanda aka kashe.
Yawancin dai wadanda aka kashen a harin fararen hula ne wadanda ba su dauke da makami, wadanda kuma aka sassare da adda da gatari yayin da wasu aka harbesu da bindiga.
Rashin tsaro a gabashin Kwango ya yi muni
Daman dai al'umma a yankin na gabashin Kwango suna cikin wani hali mummuna na rashin tsaro. Tuni dai gwamnatin ta Kwango ta dora alhakin harin a kan kungiyar 'yan tawaye ta ADF na Yuganda masu da'awar yin jihadi. Lambert Mende shi ne ministan yada labarai kana kakakin gwamntin Kwango.
Ya ce: ''Yanzu yanzu hukumomin yankin sun gano cewar mayakan kungiyar ADF sanye da kayan sojoji da ke kama da na dakarun Kwango suka kai harin. Tuni aka cafke biyu daga cikin maharan, kuma muna ci gaba da yin bincike amma karara take 'yan ta'adar ADF suka kai harin.
Kungiyar 'yan tawayen ta ADF wanda akasarinsu Musulmi ne wacce aka girka tun a shekara ta 1995 na yin adawa da gwamnatin Yoweri Museveni na Yuganda, sannan kuma wadannan 'yan tawaye na ADF na da kusan irin akida daya da 'yan kungiyar Boko Haram da ke kai hare-hare a Najeriya, da Chadi da Nijar da kuma Kamaru.
Shugaba Joseph Kabila wanda ya kai ziyara a inda lamarin ya faru ya sha alwashin kara tabbatar da tsaro a gabashin Kwango. To sai dai Séverine Autesserre wata kwararra a kan sha'anin tsaro wadda kuma ke gudanar da bincike a kan yake-yake a nahiyar Afirka, wacce ke a jami'ar Kwalambiya ta ce gwamnatin ta dade tana yi wa yankin gabashin na Kwango rikon sakainar kashi.
Gwamnati ta yi fatali da bukatun al'umma
Ta ce: "Ba na tsamanin bayan wannan ziyara gwamnatin za ta mayar da hankali kacokan a kan yankin na gabashin Kwangon kamar yadda ta yi alkawari cewar za ta ba da fifiko a kai. Al'ummar yankin gabashin Kwangon an jima ana yin fatali da su, an sha yin kashe-kashe na kare dangi a yankin a 'yan watannin baya-baya nan kawai dai maganar da Kabila ya yi furci ne a baka."
Manazarta dai na kalon cewar shugaba Joseph Kabila na iya yin amfani da damar da ake ciki ta rikicin na gabashin kasar domin kara dage zaben shugaban kasar da za a yi, wanda har yanzu ba a da tabbas dangane da ranar yin sa kamar yadda wata mai fafutuka Emery Damien Kalwira ta sanar.
Ta ce: "Shugaba Kabila yana son yin amfani da halin kashe-kashe da ake samu a wannan yanki na Kwango don ya kai ga kafa dokar ta baci, abin da zai sa ya wuce wa'adinsa na mulki har bayan shekara ta 2016 domin yin tazarce duk kuwa da kashedi da muka yi masa na cewar ya fuce daga mulkin."