1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Christian ya rasa ransa a kungiyar IS

November 6, 2018

A lokacin ya na da shekaru 27 a duniya da shi da matarsa Yasmina suka yanke shawarar shiga kungiyar IS. Shi dai Christian ya kasance mai hazaka amma yarantarsa na tattare da cece-kuce

https://p.dw.com/p/37jd2
Sabine Lappe
Hoto: DW/E. Felden

Christian da ne abin so ga mahaifiyarsa Sabine Lappe. Sai dai daga baya wannan yaro ya rikide ya zama dan ta'adda da ya sadaukar da ransa ga kungiyar IS a kasar Siriya. Mahaifiyarsa ta amince ta yi hira da tashar DW inda ta dan ba da takaitaccen tarihin abin da ya faru da dan na ta.

Sabine Lappe mai shekaru 50 da ke zaune ne a birnin Dortmund na yammacin Jamus, ta rasa danta ga kungiyar IS.

Ta ce: "Da sanyin safiyar wata ranar Asabar a shekarar 2015 an bugo min waya, na ji haushi domin ban san wanda zai bugo min waya a wannan safiya ba. Amma sai na ji muryar da-na Christian wanda kafin ranar na yi kwana biyu ban sa shi ido ba, ya ce da ni suna a Turkiyya suna jiran motar da za ta kai su Siriyya, na yi kokarin in shawo kansu amma ya ce za su tafi inda ake daukaka kalmar Ubangiji."

Syrien Christian Lappe IS Kämpfer
Mayakin IS Christian Lappe Hoto: privat

Ya yi fama da rashin lafiya an kuma yi masa aikin tiyata da yawa. Bayan ya samu lafiya ya ce dole ya godewa Allah da Ya ba shi dama ta biyu ta rayuwa. A matsayinsa na dan Katholika bai taba tunanin zama dan Salafiyya ba. Ya koma makaranta duk a kokarin kyautata rayuwarsa. A nan ne kuwa ya hadu da wasu matasa Musulmi 'yan kasashen Maroko da Turkiyya, da bisa ga dukkan alamu sun burge shi. Daga nan ya yanke shawarar karbar addinin Musulunci a cewar mahaifiyarsa.

Ta ce: "Rana guda Christian ya zo gida da kasidu a hannunsa ya ce ya yanke shawara zai karbi addinin Muslunci. Sai dai na ga alamar ya fara samun ra'ayi mai tsauri, domin idan muka fita kasuwa ba ya son ya ga na musafaha da najimi. Ya kan ce ai haramun ne."

Hakan dai ya faru ne a 2012 ita kanta Sabine Lappe ta shiga mawuyacin hali saboda mutuwar abokin zamanta ba zato ba tsammani. Ita ma ta nemi mafita. Ganin danta ya karbi Musulunci yana kuma farin ciki da haka, hakan ya sa ta fara nazari neman kusanci da addinin na Musulunci.

A karshe ita din ma dai ta Musulunta, tana kuma yawaita zuwa masallaci tare da danta. Sai dai a cewarta ita mai sassaucin ra'ayi ce.

A 2014 danta ya hadu da wata matashiya musulma 'yar asalin kasar Maroko mai shekara 17 wadda daga baya suka yi aure.

Ta ce: "Yana matukar son yarinyar domin ta karbe shi yadda yake duk da rashin koshin lafiyarsa da yawan zuwa asibiti da dai sauran dawainiya da ake masa."

Syrien Christian Lappe IS Kämpfer
Christian Lappe na kungiyar ISHoto: privat

A 2015 ma'auranta sun gudu zuwa Siriya inda suka shiga kungiyar IS. Christian na yawaita bugawa mahaifiyarsa waya. A ranar 1 ga watan Agustan 2017 ya kira ta ya ce zai koma fagen yaki. Daga na ba ta sake jin duriyarsa ba.

Ta ce: "A ranar 19 ga watan Satumban 2017 Yasmina ta bugo ta ce Christian ya yi shahada wato wanda ya mutu kenan a jihadi. Amma a gareni Christian bai mutu ba saboda bai yi jihadi don Allah ba, ya mutu ne a matsayin mayaki saboda Al-Baghdadi."

A karshen 2017 matar Christian, Yasmina ta haihu da namiji a yankin IS da aka daidaita. Ita kuma Yasmina ta auri wani dan IS dan kasar Iraki kamar yadda tsohon mijinta ya bar wasiyya.