Sabon bincike kan kwayar cutar Zika
March 1, 2016Talla
Sakamakon wani binciken kimiyya da cibiyar bincike ta Pasteur da ke a birnin Paris na kasar Faransa ta wallafa a wannan Talata a jaridar The Lancet ta Birtaniya, ya nunar da cewa akwai yiwuwar kwayar cutar Zika wacce ake fama da ita a yankin Kudancin Amirka da ke haddasa haifar jariri da nakasa ta kasance ummulhaba'isan haddasa cutar Guillain-Barre da ke kama jijiyoyin jikin dan Adam.
A cewar Parfesa Arnaud Fontanet jagoran cibiyar nazarin cututtukan annoba ta Pasteur, sakamakon binciken da suka yi kan kwayar cutar ta Zika ya nunar da cewa akwai alaka sosai tsakanin kwayar cutar da zika da kuma wannan matsala ta daskarewar jijiyoyin jikin dan Adam.