1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya kashe mutane Somaliya

Abdul-raheem Hassan
December 28, 2019

Wani kaftin na soja ya tabbatar da cewa maharan sun tarwatsa bam din da ke jikin wata mota da niyyar tarwatsa cibiyar tattara kudaden harajin kasar da ke birnin Mogadishu.

https://p.dw.com/p/3VQOi
Somalia Anschlag in Mogadishu
Hoto: Getty Images/AFP/A. Hussein Farah

Alkaluman baya-bayannan na cewa kusan mutane 90 ne suka mutu sama da mutane 50 sun jikkata a sabon harin bam da bata gari suka kaddamar a lokacin da ma'aikata da sauran jama'a ke zirga-zirga a Mogadishu babban birnin kasar.

Gwamnatin Somaliya ta ce wannan hari na cikin hare-hare mafi muni da kasar ta fuskanta a shekarun baya-bayannan. Babu kungiyar da suka dauki alhakin harin nan take, amma kungiyar al-Shabaab mai alaka da al-Qaida ta sha kai makamancin wannan hari a ciki da wajen kasar ta Somaliya.