Harin ta'addanci ya hallaka mutane a Siriya
June 11, 2016Talla
Gidan talabijin din kasar da kuma masu fafutuka da ke marawa 'yan adawa baya, sun tabbatar da faruwar harin wanda ke zama na baya-bayan nan mafi muni da aka kai a kan yankin da Musulmi mabiya mazhabar Shi'a ke da zama. Tuni dai kungiyar 'yan ta'addan IS da ta addabi kasashen Siriya da Iraki, wadda kuma ke neman zama annoba a duniya ta dauki alhakin kai harin wanda aka kai shi a hubbaren Sayyada Zainab AS. Kungiyar ta IS ta sanar da hakan ne ta kamfanin dillancin labaranta mai suna Aamaq, inda ta ce harin guda uku ne, biyu mutane ne suka yi jigida da bama-bamai, suka kuma tarwatsa kansu cikin mutane, yayin da mutum na ukun kuma ya kai harin da mota makare da bama-baman.