1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran Anschlagspläne

October 14, 2011

Zargin da Amurika ta yi wa Iran na kitsa maƙarƙashiyar hallaka jikadan Saudiya a Washington na ɗauke da barazanar ɓarkewar yaƙi.

https://p.dw.com/p/12sKp
Hoto: WILLIAM B. PLOWMAN, MEET THE PRESS

Ranar 11 ga wannan wata da muke ciki, Ministan shari´ar Amurika da shugaban hukumar leken asiri ta FBI, suka ba da labarin bankaɗo wata makarkashiya da gwamnatin Iran ta kitsa, domin hallaka jikadan ƙasar Saudi Arabiya dake birnin Washington.

Ƙsar Amurika ta yi kira da babbar murya ga ƙasashen duniya su ƙara tsuke takunkumin ladabtarwa ga hukumomin Iran, domin su gane kurensu ga wannan aika-aika.

Gwmanatin Barack Obama ga alamu ta bi sahun gwamnatin da ta shude ta tsofan shugaban kasa George Bush, wadda bisa zargin karya ta abkawa ƙasar Irak da yaƙi.

A lokacin Amurika ta kafe kan bakanta na cewar Saddam Hussein ya mallaki makamakan kare dangi, amma kuma daga bisani aka gano cewar wannan batu ba shi da kanshin gaskiya.

A wannan karon, bayan zargin da fadar White House kewa Iran na mallakar makaman nukiliya, kuma ta ce hukumomin Teheran sun dauki wani sojan haya, dilan safarar miyagun kwayoyi dan kasar Mexiko, domin ya hallaka jikadan Saudiyya dake kasar Amurika.

Saudi Arabiya na da mahimmancin matuka ga Amurika domin kasashen biyu suna cinikiyya mai karfi ta fannin man fetur da kuma makamai. Manufar shugaba Barack Obama ita ce ya nunawa Saudi Arabiya mugunyar aniyar shugaban juyin juya hali na kasar Iran Ayatollah Khameini da shugaban kasa Mahmud Ahmadinejad.

To sai dai shugaba Bush ma, a cikin kakkausan lafazi da ya fi na Barack Obama zafi, hakan ya fara zargin Irak a shekarar 2003.

Ita ma Sakaratiyar harkokin wajen Amurika Hillary Clinton, da kuma Antony Janar Erik Holder, sun shiga fadakarwa game da barazanar Iran ta fannin makaman nukiliya da kuma wajibcin daukar matakan riga kafi.

Halin da ake cikin yanzu tsakanin Amurika da Iran na tattare da hadari, babu mamaki Amurika ta dauki matakin kai hari domin wargaza tashoshin nukuliyar Iran wanda take zargi da sarrafa makaman kare dangi. To sai dai wannan mataki idan ya tabbata ba zaiwa duniya dadi ba, mussamman a cikin wannan lokaci na rikita rikita a yankin Gabas ta Tsakiya , da kuma matsalolin kariyar tattalin arziki da ta zama ruwan dare.

Magana zara bubu ce, kalamomin da Sakatariyar harkokin wajen Amurika da Ministan shari´a da kuma shugaban hukumar leken asiri ta FBI ke ambatawa yanzu game da Iran tamkar sun yi setin Iran ne da makamai. Babu shakka wannan kalamomi zazzafa suna da hadari kuma ba ta kamata a ce suna hitowa daga bakin jami´an gwamnati Barack Obama ba, mutumin da ya samu kyautar Nobel ta zaman lafiya.

Ko dai mi ke faruwa, kamata ta yi shugaba Barack Obama ya ɗauki darasi daga magabacinsa George Bush.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
dita: Mohammad Nasiru Awal