1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Falasdinu ta tsayar da yarjejeniyar tsaro da Isra'ila

Mahmud Yaya Azare ZMA
January 27, 2023

Falasdinu ta sanar da jingine aiki da yarjejeniyar tsaron hadin guiwa da 'yan sandan yankin ke yi da na Isra,ila, don tabbatar da tsaro a yankunan.

https://p.dw.com/p/4Mo6A
Westjordanland | Jenin nach israelischer Militäroperation
Yankin da sojin Isra'la ta lalata a JeninHoto: Raneen Sawafta/REUTERS

Kamar dai yadda kakakin hukumar Falalsdinawan Nabeel Abu Radeenah ke fadi, Falasdinawan sun dauki matakin katse alakar samar da tsaron hadin guiwa da Isra,ila ne,saboda irin kisan kiyashin ba gaira ba dalilin da take wa al,ummar Falalsdinawa,biyo bayan wani samame da dakarun Isra,ila suka kaddamar da ya kai ga halaka mutane goma a yankin Jenin, cikinsu har da wata tsohuwa.

  "Sakamakon la,akari da irin yadda Isra,ila ke ci gaba da cin zarafin al'ummarmu ta Falalsdinawa da kuma karya dokar da take baji ba gani, mun dakatar da ayyukan samar da tsaron hadin guiwa da ita a yankunan Falalsdinawan da take mamaye da su."

Wannan matakin dai ya biyo bayan wani samame ne da dakarun Isra'ila suka kaddamar yankin Janin da ke yankin Yamma da Gabar kogin Jodan,da nufin kakkabe wasu miyagun yan ta'adda da suke kitsa kaiwa 'yan Isra'ila hari, inji ministan tsaron na Isra,ila mai matsanancin ra'ayi Bin Gvir:

Konflikte im Westjordanland
Tafiya jana'zar wadanda somamen Isra'la ya kashe a JeninHoto: Ahmed/Ibrahim/APA/IMAGO

"Jaruman dakarunmu na aiki ba dare ba rana don bankado yan ta'adda da hana su aiwatar da miyagun nufinsu. A shirye muke mu daga duk wani dutse ko shiga ko wane sako don murkushe su da gama musu aiki."

'Yan jaridu da shedun gani da ido dai sun siffanta wannan samamen da mafi muni cikin shekaru da aka kaddamar kan yankin,kamar yadda wannan 'yar jaridar ta tashar Alarabiya ke fadi:

"Wannan shi ne famaki mafi muni mafi zubar da jinni a 'yan shekarun nan a wannan yankin. Kusan illahirin gidajen da motocin da ke kan tituna zuwa gidan da dakarun Isra,ila ke kai farmakin duk an rurrursasu. Shi kansa gidan an yi mar raga raga da harbin rokoki, gawarwakin da ake zakuluwo duk sun kone kurmus."

Westjordanland | Jenin nach israelischer Militäroperation
Wuraren da aka kai somameHoto: Raneen Sawafta/REUTERS

Ministan Lafiyar Falasdinu ya ce, baya ga mutanen 10 da suka kwanta dama, har ila yau akwai wasu 20 da suka samu raaunuka. Tun lokacin da ta fara tattara alkaluman kisa a yankin Yamma ga Kogin Jordan a shekarar 2005, Majalisar Dinkin Duniya ba ta taba samun alkaluman kisa masu yawa a sanadiyyar wani samame na rana guda ba  kamar wannan da aka yi a wannanAlhamis (26.01.23). 

Tuni dai kungiyar Hamas ta Falasdinawa da kuma kungiyar Islamic Jihad suka harba daruruwan rokjoki kan Isra,ila don mai da martini ga abun da suka kira kisan kiyashin da Isra,ila ke wa Falasdinawa, a yayin da su ma jiragen yakin Isra,ila sukai ta lugudan wuta a safiyar wannan Juma'a kan yankin Gaza da ke hannun ikon kungiyar ta Hamas.