SiyasaAfirka
Sojojin Azerbaijan sun kai hari Armeniya
September 13, 2022Talla
Jim kadan da soma kai wa kasar hare-hare, firaiministan kasar Armeniya Nikol Pashinyan ya yi kira ga manyan shugabanin duniya da su gaggauta daukar matakin ladabtar da makwabciyar kasar Azerbaijan a sakamakon kutsa kai da rundunar sojinta suka yi a yankunan kasarsa.
Pashinyan ya sheda wa shugabanin kasashen Faransa da Rasha da kuma sakatare harkokin wajen Amirka ta wayar tarho, irin barazanar da kasar ke ciki a yanzu. Rikicin wadannan kasashen biyu da suka kasance tsoffin kasashen tarayyar Soviet, ya samo asali kan yankin nan na Nagorno-Karabakh da suke jayayya akai duk da cewa an san yankin a matsayin wani bangare na Azerbaijan amma yankin na a karkashin kabilun Armeniya.