1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici ya barke a Sudan ta Kudu

Abdourahamane Hassane
April 13, 2022

An ba da rahoton cewar mutane kusan dubu 14 ke kokarin tsrewa daga yankin kudancin Sudan ta Kudu domin gujewa barkewar wani sabon tashin hankali.

https://p.dw.com/p/49tmw
Uganda Flüchtlingslager Palorinya Südsudan
Hoto: DW/L. Emmanuel

Mutanen na ficewa ne sakamakon yadda aka kwashe kwanaki biyar ana gwabza fada tsakanin dakarun mataimakin shugaban kasar Riek Machar,da na magabtansa da suka bi bayan sahun shugaba Salva Kiir a garin Leer da ke a kudancin kasar inda nan ne mahaifar Riek Mashar. Wani shaidu ya shaida wa kamfanin dilamcin labaran na Faransa AFP cewar sojojojin sun kai harin a kauyukansu suka kona gidaje tare da kwashe shanu da awaki. A cikin wata sanarwa da ya bayyana wakilin MDD a Sudan ta Kudu ya ce an wawashe kauyuka da dama da ke kudu da garin Leer da kuma  lalata tashar jiragen ruwa ta Adok da ke a kan gokin Nilu, sai dai bai bayyana wanda ke da alhakin yin haka ba.