Sabon salon harkokin siyasa a Pakistan
November 27, 2007Talla
Shugaba Musharraf na Pakistan ya fara rangadin ban kwana ga cibiyoyin sojin ƙasar, a matsayinsa na kwamandan rundunar sojin ƙasar. Rahotanni sun ce Mr Musharraf zai ziyarci cibiyar sojin ƙasar ne dake Rawalpindi, don halartar wani biki na musanman da aka shirya ma sa. Haka kuma shugaban na Pakistan zai gana da wasu ƙusoshin sojin ƙasar, a lokacin wannan ran gadi. Ziyarar dai ta biyo bayan shirin shugabanne na ajiye muƙamin shugaban rundunar sojin ƙasar ne. A gobe laraba ne a hukumance , shugaba Musharraf ke ajiye muƙamin na sa, tare da zamowa shugaban ƙasa na farar hula. A dai ranar 8 ga watan Janairun sabuwar shekara ta 2008 ne aka shirya gudanar da zaɓe na gama gari, a ƙasar ta Pakistan.