Sabon salon matakan tsaro a Burundi
July 22, 2016A cikin wannan tsari dai, a kowa ne gida za a sayi wasu kundaye guda biyu wanda a cikinsu kowane mai gida zai rubuta bayannai kan wadanda ke zaune cikin gidan, da kuma duk wata ziyara da wani ya kawo cikin gidan da madalilin kawo ziyarar. Batun kundayen dai batu ne da ya dade ana yinsa a wannan kasa ta Burundi, sai dai a wannan lokaci hukumomin sun kara tsaurara matakin, abun da ya haifar da cece kuce a tsakanin 'yan kasar kuma a cewar François-Xavier matakin ya na da kyau.
" Lalle ya kamata cikin kowanne iyali a samu wannan kundi na rubuta bayanai domin a san wadanda suke rayuwa a cikin gidan, kuma idan wani ya kawo ziyara a san dalilin ziyarar tasa."
Kundin na da tsada
Kundi daya dai ana ajiye shi ne ko yaushe a cikin gida, yayin da dayan kuma zai kasance a hannun hukuma. Sannan ana sayan kowanne daya a kudi kimanin 2000 na kasar ta Burundi, farashin da tuni wasu ke ganin tsadarsa. Sai dai a cewar Francois- Xavier, bai kamata a dubi yawan kudi ba, idan har wannan mataki zai kawo inganta tsaro tsakanin al'umma.
A baya dai ana sayen kundin rubuta bayanan ne a kasuwa, amma kuma yanzu hukumomi suka tilasta sayen wadannan kundaye a hannunta, tare da kara masa kudi. Gabriel Banzawitonde wani manazarcin harkokin yau da kunlum, na ganin cewa wannan mataki na bukatar dubawa ganin halin matsin tattalin arzikin da al'ummar kasar ke ciki.
Yarjejeniya kan sabon salon tsaro
Duk da nuna adawar da wasu 'yan kasar ta Burundi ke yi kan wannan tsari, matakin na daga cikin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin majalisar tsaron kasar ta Burundi da kuma shugabannin kananan hukumomi dan ganin ko wane dan kasa ya kawo tashi gudunmawar a fannin samar da tsaro.