1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sabon shugaban Senegal ya nada ministoci 25

Binta Aliyu Zurmi
April 6, 2024

Sabon shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya nada sabbin ministocin 25 a jiya juma'a.

https://p.dw.com/p/4eUY2
Senegals neu gewählter Präsident Bassirou Diomaye Faye
Hoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Nadin ministocin da ke zuwa kasa da mako guda bayan ya sha rantsuwar kama aiki, An nada Birame Souleye Diop a matsayin ministan makamashi, sai tsohon mai shigar da kara a kotun daukaka kara da ke Dakar Ousmane Diagne a matsayin ministan shari'a. 

kazalika daga cikin sabbin ministocin akwai mata hudu daya an nada ta ministar harkokin kasashen ketare da ta ma'aikatar kamun kifi  sai ministar iyali da matasa da kuma ta al'adu.

A ranar Talatar da ta gabata ce sabon shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye, ya nada babban jagoransa Ousmane Sonko a matsayin sabon firaministan kasar, bayan ya sha rantsuwar kama aiki.

Senegal wacce ke fuskantar kalubalen rashin aikin yi a tsakanin matasa da kusan kaso 20 cikin dari, Shugaba Faye ya ce gwamnatinsu za ta mayar da hankali wajen bai wa matasa aiki da rage farashin kayayyaki masarufi a kasar da ke yammacin Afirka gami da kare yancin bil Adama.