1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

090610 Iran Sanktionen

June 10, 2010

Ƙasashen duniya sun mai da martani bisa azawa Iran ƙarin takunkumin dunƙufar da ita

https://p.dw.com/p/NmwA
Mahmoud AhmadinejadHoto: AP

Kamar dai dama yadda aka zata, kwamitin sulhu na majalisar Ɗinkin Duniya ya sake azawa ƙasar Iran wani sabon takunkunmi, inda sabon takunkumin zai fi shafar bangaren kuɗi na jamhuriyar ta musulci.

Wannan takunkumin dai shine na huɗu wanda majalisar ta ɗorawa ƙasar Iran, tun lokacin da ta fara takun saƙa da ƙasashen yamma. Kuma ƙasashen Turkiya da Burazilne kawai suka kaɗa ƙuri'ar rashin amincewa, daga cikin dukkan ƙasashen 15 dake cikin kwamitin sulhun, sai ƙasar Lebanon wanda ta yi rowar ƙuri'arta. Ƙasar Turkiya dai ta yi Allah wadai da wannan takunkumin, haka ma ƙasar Burazil, inda jakadiyarta a Majalisar ta Ɗinkin Duniya take cewa.

"Bamu ga wani alamar cewa takunkumi wani mataki ne da ya dace a wannan taƙaddamar ba. Takunkumin kan talakawan Iran ne kawai zai yi tasiri. Daɗin daɗawa ma zai baiwa waɗanda basa son ci gaba da tattauna wata dama. Darasin da muka gani a baya, shine takunkumin yakan ƙarene da wani sakamako marar kyau, kamar yadda tafaru a ƙasar Iraƙi"

Ƙasar Jamus dai ta taka mahimmiyar rawa wajen azawa Iran sabon takunkumin, don haka jakadan ƙasar ta Jamus a Majalisar Peter Wittig, yace fatarsa itace Iran ta koma bisa tattaunawa da ƙasashen yamma.

"Yanzu muna fatan ƙasar Iran za ta miƙa wuya, domin a koma ga tattaunawa bisa shirin ta na mallakar nukiliya"

Ita kuwa ƙasar Amirka wanda itace kanwa uwar gami a tsarawa da rubuta abinda takunkumin ya ƙumsa, shugabanta Barack Obama ya bayyana irin tasirin da takunkumin zai yi a kan jamhuriyar ta musulunci, Obama yace

"Zai taƙaita ayyukan nukiliyar Iran da makamanta masu linzami. Kuma akaro na farko takunkumin ya shafi ruddunar sojin ƙasar. Kana zai karya bankunan Iran da duk wani fannin hada hadar kuɗi"

Shi kuwa shugaban ƙasar Iran Mahmud Ahmadinejad, ya kwatanta wannan sabon takunkumin a matsayin wata takardar share majina, wanda babu inda za'a jefata illah a kwandon shara. Sai yace

"Kwamitin sulhun na Majalisar Ɗinkin Duniya basu da wata alama ta demokraɗiyya, ƙasashe ne kwai dake son hawan kujerar naƙi, domin su mallaki duniya. Matakin nasu wani babban kuskure ne"

Ita dai ƙasar Iran ko a yau ɗinnan, ta bayyana cewa babu wani mahaluƙi ko kuma wai wani takunkumi, da zai sa ta bar iganta yuraniyum ɗinta. Hakama batun takunkumin ya ƙara haɗa kan 'yan ƙasar, inda ɗaukacin jaridun ƙasar ta Iran masu goyon bayan gwamnati da masu adawa duk suka yi Allah wadai da matakin na ƙasashen yamma.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Muhammad Nasiru Awal