Sabon yunƙurin ceto takardar kuɗin Euro
September 6, 2012Kwamishinan kula da harkokin tattalin arziƙi na tarayyar Turai Olli Rehn ya bayyana cewar matakan da babban bankin Turai ya ɗauka na tallafawa ƙasashen Turai da ke yin amfani da takardar kuɗin Euro za su taimakawa masu zuba jari samun gamsuwa ga irin matakan da ƙungiyar ke ɗauka na warware rikicin kuɗin da wasu ƙasashen Turai ɗin ke fama da shi, amma ya ce akwai buƙatar gwamnatoci su matsa ƙaimi wajen ci gaba da aiwatar da matakan da suke ɗauka.
Ya ce kamata yayi shirin da babban bankin Turai ya ɓullo da shi na sayan takardun shaidar zuba jari na gwamnatoci ya taimaka wajen ƙarfawa masu zuba jari gwiwar ci gaba da harkokin su, ko da shike kuma bayan bayyana matakan, Jamus ba ta yi wata-wata ba wajen yin suka game da ɗaukar su, amma bankin Turai ya ce bai saɓawa hurumin daya ke da shi ba.
Tunda farko dai gwamnan babbsan bankin Turai Mario Draghi jaddada buƙatar gwamnatoci su ci gaba da yin huɓɓasar shawo kan rikicin kuɗin ne ya yi:
Ya ce " Domin sake gamsar da masu zuba jari, akwai buƙatar magabata a ƙasashen Turai su ci gaba da aiwatar da kasafin kuɗin da Turai ta amince da su sau da ƙafa da kuma samar da sauye sauyen da za su bunƙasa gogayya a tsakanin kamfanoni da kuma gina cibiyoyin Turai."
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou