1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabunta kawancen Masar da Indiya

June 25, 2023

A karon farko cikin shekaru 20, Firaiministan Indiya Narendra Modi ya ziyarci kasar Masar don farafdo da alakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/4T2nt
Abdel Fattah al-Sisi da Narendra Modi
Hoto: Egyptian Presidency Media Office/AP/picture alliance

Mr. Modi ya gana da takwaransa na Masar Moustafa al-Madbouly da kuma Shugaba Abdel Fattah al-Sisi inda suka cimma yarjejeni a fannin sadarwa da sarrafa magunguna da cinikin makamashi da kuma yawon buda ido.

Dama dai kasar Indiya na a matsayin na bakwai a jerin kasashe abokanan huldar Masar, inda ko a shekarar 2022 kashashen biyu sun yi ciniki a tsakaninsu na akalla miliyan shida da dubu dari hudu na kudin yuro.

Firaiministan na Indiya Narendra Modi, ya gayyaci Shugaba al-Sisi domin halartar taron kasashen masu karfin masana'antu na G20 da za a gudanar a watan Satumba mai zuwa a Indiya.