Sabuwar cuta ta bulla a China
January 18, 2020Talla
Amirka ta shirya binciken ne a kokarin maganta yaduwar cutar wadda ya zuwa yanzu ta kashe mutane biyu wasu da dama kuwa ke fama da ita a China.
Cutar dai ta dauki hankalin kasashen duniya, koda yake har yanzu ba kai ga tantance ta ba.
Cibiyar da ke yaki da cututtuka ta Amirkar, ta ce gwajin yanayin zafin jikin masu shiga kasar ne tare da neman sanin wasu alamun matsalolin lafiya da suke ji suke yi.
Cutar ta kuma bulla ne a wani birnin da ake kira Wuhan a kasar ta China.
Kimanin mutum dubu biyar ne za a a bincike su daga cikin wadanda ake sa ran za su shiga Amirkar daga yankin da matsalar ta bulla a kasar ta China.