1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan ceto tattalin arzikin Girka ya samu tagomashi

mohammad Nasiru Awal/LMJJuly 17, 2015

Da gagarumin rinjaye a wannan Jumma'a Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta amince da mataki na uku na shirin ceton tattalin arzikin kasar Girka.

https://p.dw.com/p/1G0os
Kada kuri'ar amincewa da ceto Girka
Kada kuri'ar amincewa da ceto GirkaHoto: Getty Images/AFP/T. Schwarz

Wannan dai ya bude sabuwar kofar tattaunawa da nufin kare kasar ta Girka daga talaucewa. Da farko dai sai da bangarori daban-daban na wakilan jam'iyyu a majalisar dokokin suka tabka zazzafar mahawara game da shirin ceton mai sarkakiya. Norbert Lammert shine shugaban majalisar dokokin Jamus ta Bundestag lokacin da yake bayyana sakamakon kuri'ar da aka kada a wani zama na musamman da 'yan majalisar dokokin suka yi a wannan Jumma'a ya ce:

Shugaban majalisar dokokin Jamus Norbert Lammert
Shugaban majalisar dokokin Jamus Norbert LammertHoto: Getty Images/AFP/J. Macdougall

''Yan majalisa 439 sun amince, 119 sun nuna rashin amincewa, kana 'yan majalisa 40 sun yi rowar kuri'arsu."

Kada kuri'a domin neman mafita

Kuri'ar ta biyo bayan wata mahawara mai sosa rai inda aka yi ta sukar lamirin gwamnatin Girka bisa yadda ta tinkari rikicin kudin da kuma yadda gwamnatin Jamus ke jagorantar tattaunawa da Girkar. Amma babban burin da mafi rinjayen 'yan siyasar na Jamus suka sa gaba shi ne ci gaba da samun hadin kan Turai. Sai dai duk da amincewa da gagarumin rinjayen da shirin ceton tattalin arzikin Girkan ya samu, kashi daya cikin biyar na 'ya'yan jam'iyyun hadin guiwa na CSU/CDU ne suka yi wa Shugabar Gwamnatin Jamus din Angela Merkel rowar kuri'unsu.

Kalubale yayin bikin ranar haihuwa

Tun da farko Shugabar Gwamnatin ta Jamus Angela Merkel, wadda gabanin mahawarar 'yan majalisar dokoki suka ba ta furannin taya ta murnar cikarta shekaru 61 a wannan Jumma'a, ta amsa cewa mataki na uku na shirin tallafin wani abu ne mai matukar wahala ga Girka da kuma masu ba ta rance.

Ta ce: "Na san cewa da yawa daga cikinku na da shakku da kuma damuwa ko wannan hanyar za ta samu nasara, ko kasar Girka na da karfi na din-din-din na bin wannan hanya. Ba wanda zai iya kawar da wannan damuwar. Amma zai zama babban kuskure da rashin hangen nesa idan akalla ba mu jarraba wannan hanya ba.

Taya shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel murnar ranar haihuwarta
Taya shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel murnar ranar haihuwartaHoto: Getty Images/S. Gallup

A nasa bangaren ministan kudin Jamus Wolfgang Schäuble ya ce shirin tattaunawar kan mataki na uku na shirin ceto ga Girka, na zama dama ta karshe ga kasar ta Girka ta fita daga kangin matsalar kudin. Su kuwa a nasu bangaren jam'iyyun adawa na Linke da kuma the Greens sun soki shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kasa taka wa ministan kudin Jamus din birki. Ita kuwa jam'iyyar SPD da ke cikin gwamnatin kawance ta amince da shirin amma ta yi kira da a yi masa gyaran fuska. A ranar Litinin da ta gabata shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da sauran shugabannin kasashe masu amfani da kudin bai daya na Euro suka amince da wani shirin tallafa wa Girka da zai ci kudi Euro miliyan dubu 85.