Sabuwar diplomasiyyar Erdogan a kasashen Afirka
December 28, 2017
A rangadin mako guda da yake yi a kasashen na Afirka, shugaban na Turkiya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi nasarar cimma yarjejeniyoyin tsaro da tattalin arziki da kasashen Chadi da Sudan da Tunusiya, yadda shugaban Sudan Umar Al-Bashir, ya amince da danka wa kasar ta Turkiya tashar jiragen ruwa ta Sawakin don farfado da ita ta zama gagarimar cibiyar hada-hadar jiragen ruwa da za ta yi gogayya da mashigin ruwan Suweiz da ke Masar da kuma birnin Dubai na Daular Larabawa. Yunkurin da Dr Bashir Abdulfattah da ke sharhi kan lamuran yankin ke hasashen zai iya kaishi ga sanya kafar wando daya da abokan hamayyarsa a yankin:
“ Yana kokarin killace kasashen Masar da Saudiya da Emirat ne, wajen kulla kawancen tsaro da na tattalin arziki da kasashen da suke tsama da su.Yunkuri ne na kassara shirin Masar da Saudiya na samar da katafariyar tashar hada- hadar jiragen ruwa a gabar kogin Maliya da suka cimma yi a watannin banyan nan. Kamar yadda yake neman dagula lamuran siyasa a wadannan kasashen na mulkin mulukiya, ta hanyar goyan bayan kungiyoyin 'Yan Uwa Musulmi a Masar da Annahdha ta Tunusiya, wadanda ke da akidar kafa daulolin Musulunci kan tsarin zabe na siyasar Musulunci.”
Masu hamayya da shugaban na Turkiya dai, wadanda ake zargin su da kulla makarkashiyar yi mar juyin mulkin da bai yi nasara ba, sun jima suna harararsa kan hankoransa na dawo da tsohuwar daular Turkiya da ake kira Daular Uthmaniyya, wacce ta rushe a shekarar 1922, daular da ta kunshi illahirin kasashen Larabawa da wasu kasashen Afirka da Asiya da ma Turai, karkashin jagorancin khalifan Musulunci daya tilo, lamarin da shugaban kasar Tunusiya, Beji Caid Essebsi ya ce, yunkuri ne da al,ummomin larabawa suka jima suna hankorin ganin ya tabbata:
“Matakan kasashenmu biyu kusan makamantan juna ne. Mun yi imani da cewa, sakar wa al,umominmu mara da ba su damar shata makomar kasarsu da kansu shi ne kadai matakin da zai sa mu ci moriyar juna a bangarorin tattalin arziki da na zamantakewa, da kuma farfado da tsohuwar alakar da ke tsakanin kasashenmu a tsawan tarihi.”
Tabo batun yin hanun rigar da ya yi da shugaban Siriya Bashar al Asad, wanda ya siffanta da shugaban kama karya da ya halaka dubu dubatan 'yan kasarsa, ya kuma gayyato kasashen Rasha da Iran ya danka musu ragamar mulkin kasar, amadadin ya dankata ga 'yan kasar, na daya daga cikin matakan da shugaban na Turkiya ya dauka a ziyarar tasa, wacce take nuna yunkurinsa na samar da wani sabon kawancen da ya yi hanun riga da masu mulkin kama karya da sarakunan mutu kan raba da ke yankin a hanu guda, da kuma juya akalar yankin don cimma muradinsu da manyan kasashen duniya irinsu Amurka da Rasha ke yi a yankin da ke zama tsohuwar daular Musulunci ta Uthmaniyya da ta wargaje.