1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamantin Jamus ta samar da dokar masu neman mafaka

Lateefa Mustapha Ja'afarFebruary 3, 2016

Majalisar zartaswar Jamus ta amince da wata sabuwar doka a kan batun 'yan gudun hijira. Dokar wadda aka bayyana ta a matsayin mai tsauri, an amince da ita ne bayan muhawara ta tsahon lokaci.

https://p.dw.com/p/1HpDM
'Yan gudun hijira da bakin haure da ke son shiga Jamus
'Yan gudun hijira da bakin haure da ke son shiga JamusHoto: Getty Images/AFP/E. Barukcic

A karkashin dokar da aka yi mata lakabi da dokar masu neman mafaka ta biyu, masu neman mafakar musamman daga Arewacin Afirka a Jamus, za su bi wasu jerin hanyoyi tare da cika wasu sharudda na musamman kafin a amince da basu mafaka a kasar. A hannu guda kuma gwamnatin ta Jamus ta ayyana masu neman mafaka daga kasashen Arewacin Afirka wato Maroko da Aljeriya da kuma Tunusiya a matsayin wadanda suka fito daga kasashen da ba bu tashin hankali.