1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amincewa da sauye-sauyen fansho da haraji a Girka

Yusuf BalaMay 9, 2016

Kimanin masu zanga-zanga 20,000 ne suka yi wata taho mu gama da 'yan sanda dan nuna kin amincewarsu da sabuwar dokar harajin, wacce 'yan adawa suka yi wa tawaye.

https://p.dw.com/p/1Ik9g
Griechenland Athen Parlament Abgeordnete Streit
'Yan majalisa a yanayi na kalubalantar juna a GirkaHoto: picture-alliance/dpa/P. Saitas

'Yan majalisar dokoki a kasar ta Girka dai sun amince da sauye-sauye da aka samar a tsarin fansho da biyan haraji a karshen mako, tsarin da ke kunshe cikin sharudan da masu ba wa kasar bashi suka gabatar a shirin ceton kasar daga rikicin durkushewar tattalin arziki. Wannan tsarin doka da ake ta kace-nace a kai da mahukuntan na birnin Athens suka amince da ita, za ta sanya rage moriyar da 'yan fansho ke samu yayin da kuma za a kara yawan haraji da 'yan kasar ke biya.

Dukkanin 'yan adawa a majalisar mai mambobi 300 sun yi wa wannan tsarin doka tawaye yayin da bangaren Syriza masu mulki suka mara masa baya. Shirin kada kuri'a kan wannan doka dai ya fuskanci fushi na al'ummar wannan kasa ta Girka inda baya ga yajin aiki da ya gurgunta lamura a kasar, kimanin masu zanga-zanga 20,000 suka yi wata taho mu gama da 'yan sanda. Wannan dai na zuwa ne gabanin taron ministocin kasashen da ke amfani da kudin bai daya na Euro a birnin Brussels da za a yi a wannan Litinin din.