An soma wasannin lig na bana
August 8, 2022An soma sabuwar kakar wasannin lig na kwallon kafa a sassan kasashen Turai. A wasannin lig na Jamus na Bundesliga, a wasan farko mai rike da kambun Kungiyar Bayern Munich ta bi Frankfurt har gida ta yi mata cin kacar tsohon keke, shida da daya, haka ita ma Mainz ta bi Bochum gida ta doke ta da ci biyu da daya a yayin da Kungiyar Freiburg ta yi irin wannan nasara na bin Augsburg gida ta doke ta hudu da nema.
Kungiyar Wolfsburg ta tashi ci biyu da biyu da Kungiyar Bremen, Kungiyar Möchhengladbach ta doke Hoffenheim ci uku da daya, ita kuwa Dortmund ta doke Leverkusen da ci daya mai ban haushi. Kana kungiyar Union Berlin ta doke Hertha Berlin da ci uku da daya, kuma wannan wasa DW ta yi sharhi kai tsaye a kansa.
A wasannin lig na Ingila da ake kira Premier League kuwa, Kungiyar Arsenal ta bi Crystal Palace har gida ta lallasa ta da ci biyu da nema, haka ma Kungiyar Chelsea ta bi Everton har gida ta doke ta ci daya mai ban haushi.
A karshen makon da ya gabata aka kammala gasar wasannin kasashe renon Ingila wato commonwealth, Australiya ta taka rawar gani sosai inda ta tserewa Ingila mai masaukin baki da kyaututuka akalla dari da sittin da biyu, daga ciki har da kyautar zinari kimanin sittin.
A daya bangaren kuwa, hukumomin kasar Sri Lanka, sun tabbatar da cewa goma daga cikin 'yan wasan kasar da ke cikin tawagar wasannin na Commonwealth a Birmingham da ke Birtaniya sun bace, inda ake zargin suna yunkurin ci gaba da zama a kasar, ba tare da komawa gida ba.
Tuni 'yan sanda Birtaniya suka gano uku daga cikin wdaanda suka bace amma babu wani mataki da suka dauka domin babu dokar da suka karya saboda suna da takardar izinin zama na visa na tsawon watanni shida. Sri Lanka na cikin tashin hankali a sakamakon zanga-zangar jama'a kan tsadar rayuwa tun bayan da tattalin arzikin kasar ya tabarbare.