Sabuwar majalisar dokokin Pakistan ta yi rantsuwar fara aiki
June 1, 2013Talla
Sabbin 'yan majalisar dokokin kasar Pakistan da aka zaba sun yi rantsuwar fara aiki a wannan Asabar, abin da ya tabbatar da mika mulki daga hannun gwamnatin farar hula a karon farko, tun bayan samun 'yancin kan kasar shekaru 66 da suka gabata. Jam'iyyar tsohon Firaministan Nawaz Sharif ta samu nasarar kujeru 176 daga cikin 342 a zaben kasar da ya gabata, kuma ana sa ran zuwa ranar Laraba mai zuwa, Sharif zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin Firaminista a karo na uku ke nan. Gwamnatin kasar ta Pakistan za ta fuskanci kalubale da suka hada da makamashi, da farfado da tattalin arziki da uwa-uba harkokin tsaro, a wannan kasa mai mutane kimanin miliyan 180.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal