1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin Amurka da Iran

October 13, 2011

Amurka na zargin Iran da yunkurin yiwa jakadan Saudiyya a kasarta kisar gilla.

https://p.dw.com/p/12r5b
Jakadan Saudiyya a Amurka Adel al-JubeirHoto: dapd

Wani yunkurin yi wa jakadan Saudiyya a Amurkan kisar gilla, mai yiwuwa ya sabawa yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya wacce ke bada kariya ga jami'an diplomasiyya a kasashen duniya, wadda ka iya yin sanadiyyan zuwan rikicin kotun kasa da kasa. Tuni dai hukumomi a Amurkan suka kama Mansur Arbabsiya wani dan asalin Iran mai rike da takardun Amurka wanda take zargi da yunkurin. Hakanan kuma tana zargin wani dan Iran mai suna Gholam Shakuri wanda ake kyautata zaton yana daga cikin dakarun kurdawa. Iran wacce ta amince da wannan yarjejeniya a shekarar 1978 ta karyata wannan zargin to sai dai Amurkan na neman ta da ta gurfanar da wadanda ake zargi kamar yadda sakatariyar harkokin wajen kasar Hillary Clinton ta bayyana

"Irin wannan aika aika yana rage darajar dokoki da kuma tanadin tsarin kasa da kasa saboda haka dole Iran ta dauki alhakin abubuwan da ta aikata"

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita          : Umaru Aliyu