Sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan
June 9, 2023Sojoji Sudan da dakarun sa-kai na RSF sun amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta na sa'o'i 24 da masu shiga tsakani na Amirka da Saudiyya suka taimaka aka cimma. Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar ta nunar da cewa, yarjejeniyar da aka sanar bayan wasu jerin wadanda ba a mutunta ta ba, za ta fara aiki a daukacin fadin Sudan daga karfe 6 na safiyar ranar Asabar.
Washington da Ryad sun nuna ''bacin ransu'' dangane da rashin mutunta yarjejeniyoyin da aka cimma a baya. Amma wannan sabuwar yarjejeniya ta zo ne kwana guda bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya kai kasar Saudiyya, wanda ya ba da tabbacin cewa Washington da Riyadh na da burin "ci gaba da hada gwiwa domin kawo kashe fadan da ake yi a Sudan".
Rikicin na Sudan ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 1,800 tare da haifar da munanan matsalar jin kai a kasar da ke zama daya daga cikin mafi talauci a duniya.