Yarjejeniyar tsaro tsakanin Mali da Nijar da Burkina Faso
September 17, 2023Sabuwar yarjejeniyar da aka yi wa lakabi da ''Liptako Gourma'' za ta ba wa kasashen uku da ke raba iyakoki damar kafa shingayen tsaro domin taimaka wa junansu kan yakin da suke da 'yan ta'adda da suka hana al'ummominsu sukuni yau da 'yan shekaru inji kanal Assimi Goita, shugaban gwamnatin mulkin sojan Mali. Yarjejeniyar ta shata cewa duk harin da za a kai wa guda daga cikin kasashen uku na nufin cewa an saka kafar wando guda da sauran kasashen, sannan kuma za su iya kawo wa junansu dauki cikin hanzari gami da yin amfani da karfin soja a duk lokacin da wani mamba na kawancen ya fuskanci barazana. Wannan yarjejeniya dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar yuwuwar kai wa Nijar hari domin kubutar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum kamar yadda kungiyar ECOWAS ta yi barazanar yi tare da taimakon wasu kasashen Yamma.