Yankin Sahel cikin mawuyacin hali
June 16, 2022Talla
A cikin rahoton da kungiyoyin suka bayyana sun ce dubarrun tsaron da kasashen ke bi, sun gaza kare lafiyar fararan hula wadanda ke ci gaba da rasa rayukansu da matsugunansu. Rashin sahihin tsarin na taro na taimakawa wajen ruguza yarda da amincewar jama'a a kan shugabannin da ke yin mulkin a cewar kungiyoyin. Rahoton ya ce addaddin fararan hula da aka kashe a hare-haren da ake dangantawa da na kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi ya kusan rubanyawa tun daga shekara ta 2020 a kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar duk kuwa da irin yada hukumomin kasashen ke zafafa kai hare-hare.