Rundunar hadakar EU da Sahel a Mali
July 15, 2020A jimlance dai sojojin Astoniya da Faransa 100 ne za su kasance zakaran gwajin dafi na wannan shiri, duk da cewa wasu manyan kasashen Turai kamar Jamus na dari-dari wajen shiga a dama da su. Kasar Faransa da ta yi wa Mali mulkin mallaka, ita ce ta yi uwa da makarbiya wajen ganin an kafa wannan runduna da ake wa lakabi da "Takuba" don taimakawa sojojin yankin Sahel yakar ayyukan ta'addanci.
A hakikanin gaskiya dai, hadin gwiwa ne na rukunin sojojin kasashen Turai da takwarorinsu na kasashen yankin Sahel da ke fama da hare-haren masu da'awar jihadi. Sai dai Gesine Weber, kwararriya a harkar tsaro a yankin Sahel, ta ce matukar kasashen Turai da suke da karfin fada a aji kamar Jamus ba su shiga an dama da su a wannan yaki da 'yan ta'addan ba, da kamar wuya haka ta cimma ruwa. Maimakon haka ma, jami'ar ta ce wannan zai zama koma baya ga manufofin ketare da kasashen Turai suka sa a gaba. Ita dai Jamus da ke zama uwa mai ba da mama a nahiyar Turai ta fito fili ta goyi bayan wannan yunkuri na Faransa na neman kakkabe 'yan ta'adda a yankin Sahel, amma ba ta taba amincewa da tura sojojinta zuwa filin daga ba. Sai dai Gesine Weber ta ce wannan ba ya rasa nasaba da al'adun kasashen biyu da kuma dangantaka da ke tsakanin Faransa da Mali. Tun lokacin da masu da'awar jihadi da tsattsauran ra'ayin kishin addini suka yi yunkurin kafa daular Musulunci a Mali, Kasashen Turai da ma na duniya suka fara kafa rundunoni domin ja musu birki tare da neman ganin bayan ayyukan ta'addanci a yankin Sahel, inda Faransa ta kafa rundunar Berkhane yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa rundunar MINUSMA, su kuma wadanda abin ya shafa kai tsaye suka kafa rundunar hadin gwiwa ta G5 Sahel. Sai dai ayyukan sojojin kawancen na tafiyar hawainiya, lamarin da ya sa 'yan ta'adda fadada ayyukansu zuwa sauran kasashe makwabta ciki har da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso.
Amma kuma Gesine Weber masaniyar yankin Sahel ta ce rundunar "Takuba" ta sha bamban da wadanda aka kafa a baya. Ba wanda ya san tsawon lokaci da rundunar "Takuba" za ta diba wajen sauke nauyin da aka aza mata, babu ma wanda ya san ko za ta iya nasarar ganin bayan ayyukan ta'addanci da matsalolin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa a yankin Sahel, duba da canja dabaru da kungiyoyin 'yan ta'adda suka kware a kai.