1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon binciken Hillary Clinton

Suleiman BabayoJuly 5, 2016

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amirka ta cire sakamakon binciken da ta yi kan Hillary Clinton kan yadda tafiyar da bayanan sirri lokacin da take sakatariyar harkokin waje.

https://p.dw.com/p/1JJjR
USA Hillary Clinton Wahlkampf 2016
Hoto: picture alliance/AP Photo/C. Burton

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amirka, FBI, ta ce babu tuhumar da za a yi wa Hillary Clinton 'yar takara a zaben shugaban kasa bisa yadda ta yi sakaci da email lokacin da take rike da mukamun sakatariyar harkokin wajen kasar, lokacin wa'adin mulkin farko na Shugaba Barack Obama.

Babban daraktan hukumar James Comey ya shaida wa taron manema labarai cewa duk da akwai yuwuwar saba dokoki, da tsananin sakaci, amma Clinton ba ta yi haka domin ta kassara aikin gwamnati ba.

A cewar ofishin da ke yi wa Hillary Clinton yakin neman zaben shugaban kasa kuskure kawai ta yi. Amma kakakin majalisar dokokin kasar ta Amirka, Paul Ryan ya ce matakin hukumar ya nuna wariya da fifika da wani misali da ba zai yi kyau ga kasar ta Amirka ba.