1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon harin 11 ga maris a Spain

March 11, 2005

Bisa sabanin yadda aka yi zato da farko ba a samu wani canji ga zamantakewa tsakanin Musulmi da takwarorinsu 'yan kasar Spain sakamakon harin ta'addancin 11 ga watan maris na shekarar bara ba

https://p.dw.com/p/Bvcn

A wata unguwar dake da dimbim baki ‚yan kaka-gida a birnin Madrid na kasar Spain, wacce ake kiranta Lavapies, a nan ne aka kama da yawa daga cikin wadanda ake tuhumarsu da laifin kai hare-haren ta’addancin 11 ga watan maris na shekara ta 2004. Akasarinsu kuwa ‚yan kasar Maroko ne, wadanda kafin wadannan hare-hare ba a hangi wata alama ta tsageranci daga garesu ba. Dangane da harkokin rayuwa ta yau da kullum dai babu wani canjin da aka samu a wannan unguwa sakamakon wadannan hare-hare da kuma kame-kamen da suka biyo baya, bisa sabanin yadda aka yi zato da farko na cewar za a shiga wani mummunan yanayi na kiyayya da gaba da kuma kyamar musulmi a duk fadin kasar Spain. Wannan kuwa wani kyakkyawan ci gaba ne a cewar wani da ake kira Mustafa El-Mirabet, shugaban kungiyar ma’aikata ‚yan usulin Morko. Amma duk da haka yana tattare da imanin cewar wadannan hare-hare sun taimaka wajen zubar da martabar Marokawa a idanun al’umar Spain. Sai ya ci gaba da cewar:

Ba zamu iya yin ko oho da tahakikanin gaskiyar cewar wasu ‚yan kasar Moroko na da hannu a wannan ta’asa ba. An tsare wasu daga cikinsu a kurkuku a yayinda ake ci gaba da farautar wadansu. Dukkan wadannan abubuwa sun canza wa Marokawa fasali a idanun al’umar Spain tare da shafa musu kashin kaza.

Wadannan lkalamai na Mustafa El-Mirabet, ba kawai suna nuna damuwa ne kadai ba, kazalika wata alama ce ta irin takaicin dake tattare a zuciyarsa. A zamanin baya ‚yan kasar ta Moroko dake ci rani a Spain su kan sha fama da gwagwarmayar neman hakkinsu, amma a yanzu an wayi gari suna fama da kyama da barazana game da makomar rayuwarsu. Domin kuwa irin wannan ta’asa ba za a iya yin watsi da ita kwata-kwata domin mayar da dangantaka kamar yadda aka saba yau da kulum ba. Akwai da yawa daga al’umar kasar Spain dake bayyanarwa a fili cewar tun bayan hare-haren na 11 ga watan maris suzka shiga daridari da musulmi. An saurara daga bakin wani dan kasar ta Spain yana mai bayanin cewar a zamanin baya su kan yi haba-haba da baki, amma tun bayan wadannan hare-hare suka rungumi akidar kabilanci da wariyar al'uma. Ba dai dukkan ‚yan kasar Spain ne ke da wannan akida ba. Domin kuwa an ji daga wani malamin makaranta dake bayanin cewar tun bayan abin da ya faru a 11 ga watan maris ya dukufa akan bincike domin fahimtar musulmi da al’adunsu, tare da saka ayar tambaya a game da musabbabin wannan danyyen aiki. A dai halin da ake ciki yanzu babban abin da gwamnatin kasar ta ‚yan socialist ta sa gaba shi ne karfafa manufofin kyautata zaman cude-ni-in-cude-ka tsakanin illahirin mazauna kasar. Kuma nan gaba za a rika koyar da darussan addinin musulunci a makarantu na gwamnati, lamarin da su kansu musulmin ke marhabin da shi.