Sakamakon taron ministocin kuɗi na ƙasashen da ke amfani da Euro
July 10, 2012A taron da suka shirya a birnin Brussels na ƙasar Beljiam,ministocin kuɗi na gungun ƙasashe masu amfani da euro wato "Eurogroup" sun amince Firaministan Luxemburg Jean Claude Junker, bugu da ƙari shugaban majalisar ministocin kuɗin Eurogroup ya cigaba da jagoranci.
Kamin cimma wannan sakamako, saida aka sha kai ruwa rana tsakanin ƙasashe masu amfani da tarkardar kuɗin Euro domin banda Jean Claude Junker akwai takarar ministan kuɗin Jamus Wolfgang Schäuble, to saidai ba ta samu haɗin kai ba daga ƙasar Faransa, ɗaya daga ƙusoshin rukunin ƙasashe masu amfani da Euro.
Bayan lokaci mai tsawo ana tafka mahauwa a ƙarshe dai ministocin kuɗin sun amince su tsawaita jagorancin Junker da shekaru biyu da rabi, to amma ya ce ba zai cika wannan wa'adi ba ya na shugabancin:
"An sake zaɓe na a matsayin shugaban komitin kuɗi na gungun ƙasashen da ke amfani da kuɗin Euro har tsawan shekaru biyu da rabi.Saidai ba ni da burin kammalla wannan wa'adin mulki.
A ƙarshen wannan shekara ko kuma idan an daɗe a farkon shekara mai kamawa zan sauka".
A ɗaya wajen, ministocin kuɗin ƙasashen Eurogroup, sun zaɓi Klaus Regling dan Jamus a matsayin wanda zai shugabacin Asusun ceto na mussamman da ƙasashen su ka girka domin kai tallafi ga takwarorinsu da ke fama da matsalolin tattalin arziki.
Ministan kuɗin ƙasar Faransa Pierre Moscovici ya yaba da sakamakon da taron ya cimma ya na cewa:
"Mun tsaida shawarwari masu inganci.Abinda ya rage yanzu shine mu ƙaddamar da su.Wannan shine karon farko da aka samun haɗin kan ƙasashen gaba ɗaya ta fannin hanyoyin fuskantar ƙalubalen tada komaɗar tattalin arziki da haɗin kan ƙasashen ƙungiyar tarayya Turai gaba ɗaya.An cimma wannan sakamako cikin fahintar juna mussamman tsakanin ƙasashen Faransa da Jamus."
Ministocin kuɗin ƙasashen Eurogroup, sun ƙara baiwa ƙasar Spain wa'adin shekara guda, domin ta aiwatar da tsarin cike giɓin tattalin arzikinta.Ministan kuɗin Jamus Wolfgang Schäuble yayi ƙarin haske game da dalilan ɗaukar wannan mataki:
"Matakai ne masu ƙarfi da ke buƙatar lokaci issashe, mu na sane da matsalolin da ke tattare da cimma wannan manufa, saboda haka cilas ne bankuna su ƙara jajurcewa."
A ɗaya wajen, Wolfgang Schäuble, ya yi hannunka mai sanda ga gwamnatocin gungun ƙasashen Eurogroup ta fannin ƙara matsa ƙaimi wajen yaƙi da almubazaranci da kuɗaɗe ta yadda za a yi riga kafi ga faɗawa cikin yanayin talauci.
Ministocin sun jaddada aniyarsu ta taimakawa Spain da tsabar kuɗi wuri na gugar wuri har Euro miliyan dubu ɗari, to saidai za su fara zuba Euro miliyan dubu talatin kamin ƙarshen watan da mu ke ciki.
A cikin nasa jawabin, shugaban babbar bankin ƙasashen Turai Mario Draghi ya yaba da cigaba da aka fara samu a ƙasashen Eurogroup da suka fama da matsalolin kuɗaɗe , wanda kuma su ka samu tallafin Asusun ceto:
"Ci gaban da muka samu ƙarara ya ke, idan ka dauki misalin ƙasashe kamar Irland ko Portugal sun yi abin azo a gani a yunƙurin hita daga ƙangin talaucin da ya mamaye su a baya, saboda haka ne ma a yanzu mu ka daina matsa masu lamba."
Duk da wannan cigaba da aka fara samu ministocin kuɗin ƙasashe masu amfani da Euro sun yanke shawara girka wani komiti na mussamman wanda zai dinga sa ido ga aiyukan bankunan ƙasashen ta yadda za a guji komawa gidan jiya noman goje.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu