1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zabe ya fara fita a Saliyo

June 26, 2023

Kwarya-kwaryan sakamakon zaben shugaban kasar Saliyo da hukumar zabe ke ci gaba da fiddawa na nunar da shugaba mai ci Julius Maada Bio a sahun gaba da kashi 55,86 cikin dari.

https://p.dw.com/p/4T5sv
Sierra Leone | Wahlen | Julius Maada Bio
Hoto: Cooper Inveen/REUTERS

Kawo yanzu kashi 60 cikin dari na kuru'un da 'yan kasar suka kada a ranar Asabar din da ta gabata ne aka kai ke kidaya wa, inda Shugaba Juluis Maada ya tashi da jimillar kuri'u 1.067.666 yayin da abokin hamayarsa Samura Kamara shi kuwa ke da kuri'u 793.751 kwatankwacin kashi 41,53 cikin dari.

Ana dai sa ran hukumar zaben kasar ta fitar da kammalalen sakamakon zaben nan da kwanaki biyu masu zuwa kamar yadda shugabanta ya alkawarta.

Zaben na kasar Saliyo dai ya kasance mai cike da tashin hankali inda aka yi ta dauki ba dadi tsakanin 'yan sanda da magoya bayan jam'iyyun adawa, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da kuma jikkatar wadansu.