Sakamakon zaben Togo
July 27, 2013Rahotanni na wucin gadi na zaben majalisar dokokin da aka gudanar ranar Alhamis din da ta gabata a kasar Togo na nuna cewa jam'iyyar da ke mulkin kasar ta shugaba Faure Gnassingbe na kan gaba da kashi sittin da shida cikin dari na kuri'un da aka kidaya.
To sai dai jam'iyyun adawa a kasar na cewar an tafka magudi kuma za su kalubalanci sakamakon zaben, da za a fidda a hukumance, amma masu sanya idanu na kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS sun ce zaben ya gudana ba tare da wani magudi ba,sai dai sun ce sun bankado wasu kurakurai nan da can.
Tuni dai jami'an ECOWAS da aka gudanar da zaben na Togo kan idonsu suka yi kira ga al'ummar kasar da su guji ta da hankali gabanin fitar sakamakon zaben na din-din-din inda suka kara da cewar kyautuwa ya yi masu korafi game da zaben su ruga kotu maimakon daukar doka a hannunsu.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita. Halima Balaraba Abbas