Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya: Fafitikar neman zaman lafiyar duniya
Rayuwa a New York, babu biyan haraji, tare da aikin neman zaman lafiyar duniya. Aiki kamar a mafarki. Yanzu an fara tattaunawa a game da neman mukamin da ya fi girma a Majalisar Dinkin Duniya. Mata za a bai wa fifiko.
Mai jawo muhawara: Irina Bokova
Daya daga cikin masu damar samun mukamin ita ce 'yar Bulgariya Irina Bokova, wadda tun 2009 take da matsayin Darekta-Janar ta UNESCO. Bokova wadda danginta masu fadi aji ne a jam'iyyar kwaminis, ta yi karatun dangantakar kasa da kasa a Moscow, inda ministan harkokin wajen Rasha Lavrov ya yi karatu. Rasha tana matsa lambar samun Janar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya daga gabashin Turai.
Tarihin rayuwa mai dan kuskure
A takardun bayaninta lokacin kama mukamin, Bokova ta baiyana kanta da sunan tsohuwar ministan harkokin wajen Bulgariya, amma ba ta taba rike wannan mukami ba. Ofishinta ya ce an sami kuskuren da babu wanda ya lura da shi, har zuwa lokacin gabatar da takardun neman mukamin Sakatare-Janar. Sai dai a karon farko a tarihin shekaru 70 na Majalisar, wannan mukami an wareshi ne ga mace kadai.
Wacce ta fi nuna alamun samun nasara
Babbar mai kalubalantar Bokova ita ce shugaban hukumar UNDP, Helen Clark, kuma ita ce ta karshe a jerin wadanda suka gabatar da takardunsu. To amma ba za ta so a zabeta kawai saboda tana matsayin mace ba."Ina son mata su ma a basu damar karbar mukami komai girmansa idan sun cancanta", inji ta. Clark tana da kwarewar shugabanci a matsayin tsohuwar Firaministar New Zealand daga 1999 zuwa 2008.
Shugabanci mai karfi, alkiblar da ta dace
Clark da ta shugabanci jam'iyyarta da hannun karfe. Babu ko shakka ita ce 'yar siyasa mafi kwarewar iya aiki a New Zealand daga shekaru 10 da suka wuce zuwa yanzu. Mafi yawan yabon da ta samu daga 'yan kasarta, ta same shi ne saboda tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa Afghanistan da Somaliya, maimakon a tura su domin shiga yakin kasar Iraki.
Ba sani, ba sabo: Vesna Pusic
Kasar Croatia ta zabi tsohuwar ministar harkokin wajen kasar, Vesna Pusic. Tun 2000 take wakiliya a majalisar dokoki, kuma ta yi takarar neman mukamin shugaban kasar ba tare da nasara ba. Pusic maaaniya a fannin rayuwar dan Adam, ta kafa kungiyar kare hakkin mata ta farko a tsohuwar Yugoslaviya a shekaru na 70, kuma tana daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar al'umma ta Croatia shekara ta 1990.
Mai kwazo da hazaka
Natalia Ghrman, tsohuwar ministan harkokin waje, tsohuwar mataimakiyar shugaban Moldaviya ba a santa sosai ba kamar sauran 'yan takara da ita. Ta yi aiki a wasu hukumomi na Majalisar Dinkin Duniya. A wata mukabala ta ce: "Ko a batun yaki da yunwa ko hana yaki ko tabbatar da hakkin jama'a ko kuma neman ceto duniyarmu, babu wani lokaci da Majalisar Dinkin Duniya ta zama mai muhimmanci kamar yanzu."
Mai yawan tunatarwa: Antonio Guterres
Antonio Guterres ya jagoranci hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya zuwa 2015 sai dai bai kammala aikinsa yadda ya so ba. Karon farko an sami 'yan gudun hijira fiye da miliyan 60 a duniya. A matsayin shugaban majalisar shawara ta kasashen Turai, ya shugabanci taron kolin kasashen Kungiyar EU da Afirka a farkon 2000. Guterres ya rike mukamin Firaministan Portugal har zuwa 2002.
Mai sassaucin ra'ayi: Srgjan Kerim
Tsohon ministan harkokin wajen Macedoniya, Srgjan Kerim ya yi aikin jakadanci har ma a nan Jamus. Daga 2007 zuwa 2008, ya jagoranci zaman babban taron mashawartar Majalisar Dinkin Duniya. A takardunsa na neman mukamin Sakatare-Janar, ya ce yana da muhimmanci a gane muhimmancin ko wane dan Adam. Yana da matukar sha'awar tsara rubutattun wakoki da daukar hotuna.
Masanin tattalin arziki: Igor Luksic
Igor Luksic shi ne mafi kankantar shekaru tsakanin 'yan takara. Ko da shi ke bai cika shekaru 40 da haihuwa ba, amma ya yi tashin gwauron zabo a aiyukansa. A 2004 ya zama ministan kudi sannan bayan 'yan shekaru ya zama Firaministan Montenegro. A kasarsa yana daga cikin masu goyon bayan kasashen yamma da kungiyar NATO. Babban sha'awarsa shi ne fannin tattalin arziki. Yana tsara rubutattun wakoki.
Kwararre: Danilo Türk
Tsohon shugaban Sloveniya Danilo Türk ya dauki lokaci mai tsawo a New York kan harkokinsa na siyasa fiye da zaman da yayi a kasarsa. Daga 1992 zuwa 2000 ya zama wakilin Sloveniya a Majalisar Dinkin Duniya, kafin Sakatare-Janar Kofi Annan ya nada shi a mukamin mataimakinsa. Masanin shari'ar ana daukarsa a matsayin mai gwagwarmayar kare hakkin dan Adam, musamman a wuraren da ake fama da yaki.
Bukatar hana boye-boye
A karshen shekara Ban Ki-Moon dan Koriya ta Kudu zai sauka daga mukaminsa bayan cika wa'adi biyu tsawon shekaru 10. Yanzu an fara matakin neman zaben majalinsa. Tun daga Talata zuwa Alhamis, 'yan takarar za su gabatar da kansu gaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya. Majalisar musamman ta fi son ganin mace a kan wannan mukami, abin da ya bai wa 'yan takara daga gabashin Turai kyakkyawar dama.
Mai neman sulhu a duniya
Sakatare-Janar yana da ma'aikata 44.000 karkashinsa, ya kan ziyarci wurare na rikice-rikice tare da ganawa da shugabannin duniya. Sai dai ba shi da karfin angizo na siyasa, ana ma iya kiransa Paparoman neman zaman lafiyar duniya. Karfin Majalisar Dinkin Duniya ya tattara ne a kwamitin sulhu, musamman kan manyan kasashe masu ikon hawa kujerar na ki: China, Faransa, Ingila, Rasha da Amirka.
Mai jiran tsammani: Angela Merkel
Wani sharhi na tsohon jami'in yada labarai na Sakatare-Janar cikin jaridar New York Times, ya yabi shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a matsayin wacce ta fi dacewa da wannan. Bayan kasancewarta mace, kuma 'yar asalin gabashin Turai, tana da fahimta da Rasha, tana kuma iya shiga tsakanin Amirka da Rasha. Masana na Majalisar Dinkin Duniya sun daidaita cewa Merkel ita ce 'yar takarar da ta dace.